Tutar da aka bayyana a Ibadan ba shi ne mafi girma a duniya ba kamar yadda kafofin yada labarai suka rawaita ba

0

Ranar Alhamis 24 ga watan Yunin 2021, babban hafsan tsaron sojojin Najeriya Janar Lucky Irabor, da wanda ya kirkiro zanen tutar Najeriya Pa Taiwo Akinwumi da iyalansa da abokan arziki da ma shahararren mawakin nan Timi Dakolo suka gabatar da abin da aka bayyana a matsayin tuta mafi girma a duniya a filin wasan Polon da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Yayin da yake jawabin marabtar baki, Akinwumi ya bayyana farin cikinsa da yadda aka karrama shi tun yana raye. “Ko da yaushe ina mafarkin Najeriya a matsayin wadda ke kan gaba a duk wani abu mai kyau.” A watan Okotoban 1959 Pa Akinwumi ya kirkiro zanen tutar da kalolinta lokacin yana da shekaru 23 kacal na haihuwa. Dattijon mai shekaru 85 yanzu, ya ce ya yi zanen tutar ne lokacin da yake karantun zama injiniya a fanin wutar lantarki a Kwalejin Fasaha ta Norwood da ke Landan.

Tantancewa

Domin gano gaskiyar wannan batu wanda da aka wallafa a jaridu da dama wadanda suka hada da jaridun Tribune, da ThisDay da The Guardian da sauransu, Dubawa ta binciki shafin yanar gizon Guinness world record, (wato shafi ko kuma littafin da ya yi suna wajen wallafa bayanan mutanen da suka yi fice a fannoni daban-daban da ma abubuwan ban mamaki a duniya baki daya.) dan ganin ko akwai bayani dangane da tuta mafi girma a duniya.

Daga nan ne muka gano cewa kasar Qatar ce ke da tuta mafi girma a duniya. Ta bayyana wannan tuta ne a shekarar 2013, lokacin daya daga cikin bukuwan ranar tunawa da Qatar wadda akan yi ranar 17 ga watan Disembar kowace shekara. Tutar mai kaloli biyu – ja da fari – ta rufe filin da ya kai girman filayen kwallon kafa guda 14 a wani yankin masana’antun da ke arewacin babban birnin kasar wato Doha.

Tutar na da nauyin tonne 9.8. Yadin da aka yi amfani da shi wajen dinka tutar sai da aka yi amfani da jiragen sama guda uku aka dauko, a cewar daya daga cikin jaridun kasar al-Sharq. A shekarar tutar ta Qatar ta ture wadda aka dinka a Romania wadda ita ce da aka sa a matsayin mafi fadi a duniya, a cikin littafin na Guinnes book of world record, a watan mayun wannan shekara.

Mun yi karin binciken da ya sake nuna mana cewa tuta mafi girma da aka taba shawagi da ita a sararin samaniya ita ma daga wannan yankin take, kuma tana da fadin 2,448.6 sq m. Kamfanoni biyu a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) suka hada gwiwa wajen cimma wannan burin a yin shawagi da tutar. Kamfanonin sun hada da Trident Support Flagpoles da Sharjah, a nan a Hadadiyyar Daular Larabawar a shekara ta 2017.

Shafin daya daga cikin jaridun Dubai mai suna Zawiya (wadda ta kasance jagora a labaran kasashen yankin da bayannan sirri, wadda kuma ma’aikata da dama ke tuntuba dan samun labarai, kama daga UAE har zuwa Saudiyya da Masar) ita ma ta karfafa bayanan da muka samu a cikin wani rahoton da ke shafinta dangane da tutar.

Kamar Qatar, gwamnatin Dubai ta yi tutar ne domin nunawa ‘yan kasa cewa suna da mahimmanci lokacin bukin tutoci na duniya a shekara ta 2017.

Haka nan kuma mun sami labarin cewa tutar na daya daga cikin manyan wuraren yawon bude ido a Shrajah wanda ake kira Flag Island a turance ko kuma tsibirin tuta. Nan ne aka sanya tutar mafi fadi a duniya (wanda aka yi shwag da ita) a kan pole din da ke da bisar mita 123. Wannan bisa yana matsayi na 7 a jerin tutoci masu bisa a duniya lokacin da aka bude wurin ranar 2 ga watan Disembar shekarar 2012.
Tutar ta shiga Guinnes World Records lokacin da aka bayyana ta a bukin da tsibirin ta shirya a matsayin bukin ranar tuta ta kasa.

Kholood Al Junaibi, manajan tsibirin tutar ya ce kasancewar tutar a wurin ya kara yawan nasarorin da tsibirin ya yi inda ya jaddada burinsu na cimma irin nasarorin da za su bayyana irin kimar da UAE ke da shi da ma Sharjah a yankin da duniya baki daya.

A Karshe

Batun cewa tutar Najeriyar da aka bayyana a Ibadan jihar Oyo ita ce wacce ta fi kowacce tuta a duniya fadi da girma a duniya ba gaskiya ba ne. Guiness World Book of Records ya ce tutar da aka bayyana lokacin bukin karrama Qatar a shekarar 2017. Tutar na da fadin 101,978 sqm yayinda na Ibadan kuma ya kasance 3,275.6.

Share.

game da Author