Kakakin rundunar Ƴan sandan jihar Kaduna Muhammed Jalige ya bayyana cewa wasu matasa sun babbake wasu da ake zargin ƴan bindiga a unguwar Kakuri dake Kaduna ranar Alhamis.
Jalige ya ce matsan sun fatattaki waɗannan mutane ne tun daga unguwar Barnawa har zuwa Kakuri inda da karfin tsiya suka buge su sannan suka dildila musu fetur suka cinna musu wuta ranar Alhamis da karfe 4 saura kwata.
Sannan kuma da aka caccaje gawarwakin waɗannan mutane da aka babbake, an tsinci wayoyi uku da bindigogi biyu tare da su.
Jalige ya ce tuni an kai gawarwakin nasu dakin ajiye gawa dake asibitin Gwamna Awan, dake Kakuri.
A karshe kakakin ƴan sandan Muhammed Jalige ya yi kira ga matasa su daina ɗaukan hukunci a hannun su. Maimakon haka su rika sanar da hukuma ko ƴan sanda.
Yin garkuwa da mutane da karɓar kuɗin fansa ya yi tsanani a jihar Kaduna.
Wasu da suka tattauna da wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA a Kaduna sun bayyana cewa duk da ya kamata matasa su sanar da ƴan sanda maimakon daukar hukunci kai tsaye tura ce ta kai bango.
” Mutane sun fara gajiya ne da kullum an kama amma ba ace ga yadda aka yi da su ba. Shine ya sa da zaran sun damke wani da ba su yadda da karauniyar sa ba sai sun zartar masa da hukunci kawai kai tsaye kowa ya huta.