Tsurku, Bita-Da-Ƙulli, Hassada da Nuƙufarcin da ake kulla min ba za su hana ni yin takarar shugabancin APC ba – Yari

0

Tsohon gwamnnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya ce ba ya tsoron masu shirya masa tuggun kada ya yi takara ko nasara a burinsa na zama shugaban jam’iyyar APC.

Yari ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja ranar Lahadi.

” Wasu daga cikin tsoffin abokan aikina da wadanda muke tare a baya na shirya min maƙarƙashiyar yadda za a hana ni takarar shugabancin jam’iyyar APC da ke tafe.

” Amma abinda nake so su sani shine ba su isa su hani yin takarar shugabancin jam’iyyar APC ba. Zan yi wannan takara kuma ba na tsoron su.

“Wani abu da ya sa ba su so in yi takarar shugabancin jam’iyyar shine wai don wasun su tsoffin gwamnoni da wadanda ke kan kujerun mulki suna so su zama shugaban kasa ko mataimaki wanda idan na zama shugaban APC daga yankin Arewa Maso Yamma, burin su ba zai cika ba.

” Amma ni abinda nake so su sani shi, ta Allah ba tasu ba, ina nan daram kuma na gama shiri tsaf zan yi takarar shugaban jam’iyyar APC, kuma ba su isa su kawo min cikas ko matsala ga abinda na saka a gaba ba.

Yari ya kara da cewa babu wani da zai nemi kujerar shugabancin jam’iyyar da ya fi shi cancanta a siyasance.

Tun daga jam’iyyar APP ake fafatawa da ni kuma muna yin nasara tun daga gida Zamfara, har jam’iyyar ta zama ANPP kafin muka zama APC. Kuma duk na bada gudunmawa masu yawa a nasarorin da aka samu tun daga wancan lokacin.

Share.

game da Author