Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya kama hanyar isa Kurkukun birnin KwaZulu Natal, inda zai yi zaman watanni 15 ɗin da Babbar Kotun Ƙolin ƙasar ta yanke masa hukunci.
An yanke wa Zuma hukuncin ne saboda ya raina kotu, bayan ya ƙi halartar gayyatar da Kwamitin Binciken Badaƙalar Kuɗaɗe a zamanin mulkin sa.
Saboda ƙin halartar, sai Babbar Kotun ta ɗaure shi watanni 15, inda ta umarce shi da ya kai kan sa Kurkukun KwaZulu Natal cikin kwanaki 5.
Ranar Lahadi da ta wuce kwanakin biyar su ka cika, amma bai kai kan sa kurkuku ba.
Sai kotu ta umarci ‘yan sanda su kamo shi ko da tsiya idan ya ƙara kwanaki uku bai kai kan sa ba, zuwa ranar Alhamis kenan.
To sai dai kuma Gidauniyar Tallafin Al’umma ta Jacob Zuma, ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar ya bi umarnin kotu, domin ya na kan hanyar zuwa kurkukun.
Lauyoyin Zuma sun buƙaci kada a tsare shi, amma kotu ta ce alƙalami ya bushe. Sai dai ya jira hukuncin da kotun za ta sake yankewa a ranar Juma’a.
Masana na ganin cewa babu makawa sai Zuma ya shafe watanni 15 a kurkuku.
Zuma shi ne shugaba na uku bayan samun ‘yanci a ƙasar. Bayan Nelson Mandela, Thabo Mbeki ya yi mulki. Daga shi sai Zuma.