TAZARAR HAIHUWA: Ana daukan cikin da ba a shirya masa ba akalla miliyan 2.5 a Najeriya duk shekara

0

Wasu jami’an lafiya sun bayyana cewa mata na daukan cikin da basu shirya masa ba akalla miliyan 2.5 a Najeriya duk shekara.

Likita da ya kware a harkar haihuwa, daukan ciki da matsalolin da suka shafi haihuwa dake aiki a asibitin UCH a Ibadan jihar Oyo Christopher Aimakhu da farfesa Abubakar Panti dake aiki a fannin kula da daukan ciki, haihuwa da matsalolin da suka shafi haihuwa a asibitin koyarwa na Usman Danfodiyo UDUTH a jihar Sokoto suka sanar da haka a taron tattauna matsalolin da suka samu tushen zama a dalilin rashin samar da dabarun bada tazaran haihuwa a kasar nan.

Kungiya mai zaman kanta ‘Rotary Action Group for Reproductive, Maternal and Child Health Nigeria’ RMCH tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya da ma’aikatar tattalin arziki da ci gaba na kasar Jamus suka shirya taron a Abuja daga ranar Laraba zuwa Alhamis

Abinda bincike ya nuna

Aimakhu ya ce Najeriya na da babban kaso daga cikin mata miliyan 190 dake duniya dake fama da karancin dabarun bada tazaran haihuwa.

Ya ce hakan ya faru ne saboda karancin dabarun bada tazaran haihuwa da ake fama da shi a kasar nan.

“Ya zama dole gwamnati da kungiyoyin bada tallafi su mike tsaye wajen samar da isassun dabarun bada tazaran haihuwa a kasar nan.

Aimakhu ya ce samar da isassun dabarun bada tazaran haihuwa zai taimaka wajen samun ragowan kashi 77% ko kuma ragin 555,000 daga miliyan 2.5 a daukan cikin da ba a shirya masa ba.

Ya kuma ce hakan zai taimaka wajen rage haihuwa ‘ya’yan da ba a shirya masu ba daga 885,000 zuwa 200 sannan da rage yawan zubar da ciki daga miliyan 1.3 zuwa 287,000.

Shi kuwa panti ya ce rashin samar da isassun dabarun bada tazaran haihuwa na cikin matsalolin da ya sa mata da dama ke mutuwa wajen haihuwa a kasar nan.

Ya ce bincike ya nuna cewa mata wadanda basu yi aure ba kashi 50% na fama da rashin samun dabarun bada tazaran haihuwa.

“Rashin samun isassun dabarun bada tazaran haihuwa ka iya sa mata daukan cikin da basu shirya ba, su haifi dan da basu shirya kula da shi ba ko kuma su je su zubar da cikin wajen wanda bai kware ba wanda hakan ka iya yin ajalinsu.

“A Najeriya sakamakon binciken da NDHS ta gudanar a shekaran 2018 ya nuna cewa mata kashi 19% ne ke fama da rashin samun dabarun bada tazaran haihuwa sannan matan da basu yi aure ba sun kai kashi 48%.

Panti ya ce ga kowani ciki da mace za ta dauka tana cikin hadarin rasa rayuwanta.

” Mata masu kananan shekaru talakawa sun fi mutuwa wajen haihuwa a dalilin rashin samun dabarun bada tazarar haihuwa.

“An yi hasashen cew za a iya ceto ran mace mai ciki daya daga cikin mata uku idan aka samar da isassun dabarun bada tazaran haihuwa.

Ware isassun kudade domin Samar da dabarun bada tazaran haihuwa a Najeriya.

Wasu kwararrun jami’an lafiya da Suka halarci taron sun yi kira ga gwamnati musamman gwamnatin jihar da su ware isassun kudade domin Samar da dabarun bada tazaran haihuwa a Najeriya.

A shekaran 2012 Najeriya ta dauki alkawarin Samar da isassun dabarun bada tazaran haihuwa domin ganin a kalla mata kashi 27% na amfani da dabarun a kasan nan da shekaran 2020.

A shekaran 2020 mata kashi 13.9 ne kadai ke amfani da dabarun bada tazaran haihuwa.

A dalilin haka ya sa gwamnati ta sake daukan wani alkawarin samar da dabarun bada tazaran haihuwa wa mata kashi 27% nan da shekaran 2024

Gaggauta Samar da dabarun bada tazaran haihuwa

Panti ya ce Samar da isassun dabarun bada tazaran haihuwa ya zama dole ganin cewa komai ya canja.

Yanzu an shigo zamanin da mutane da kansu na kokarin rage yawan haihuwa yara saboda suna da burin Samar musu ingantaciyar ilimin boko, lafiya da sauran su.

Sannan karancin ababen more rayuwa na cikin matsalolin da ka iya sa gwamnati ta fadaka wajen rage yawan mutane a kasar nan.

A karshe shugàban fannin haihuwa na ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya FMOH Kayode Afolabi ya ce gwamnati a shirye take domin ware kudaden Samar da isassun bada tazaran haihuwa wa mata a kasar nan.

Share.

game da Author