Tsohon shugaban rusasshiyar jam’iyyar CPC, Jam’iyyar Buhari, Rufai Hanga, ya bayyana cewa tabbas akwai alkawarin da aka yi tsakanin Buhari da Tinubu a wancan lokacin cewa idan Buhari ya Kammala zangon sa ta biyu zai mika wa Tinubu ne mulkin Kasar nan.
Rufai Hanga ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da Daily Trust wanda ta wallafa hirar ranar Lahadi.
” Lallai a wancan Lokacin da ake tattauna haɗewa tsakanin CPC da ACN, akwai alƙawarin yarjejeniyar da aka yi cewa idan Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa zai mika wa Tinubu mulki ne a 2023.
” Sai dai kuma akwai matsala yanzu domin akwai yiwuwar hakan ba zai samu ba. Wasu dake tare da Buhari sun kunno kai cewa ba shi ne za a baiwa mulki ba, Idan da Tinubu ya san babu irin wannan yarjejeniya, ina tabbatar muku da bai goyi bayan Buhari ya zarce a 2019 ba. wannan shine gaskiyar magana.
Hanga ya ce ya hango rudani mai zafin gaske dake kunno kai a jam’iyyar APC wanda idan ba a iya shawo kansa ba, PDP za ta ragargaji garaɓasa a 2023, domin APC din tarwatsewa zata yi, baya kuma ga gazawar wannan gwamnati na Buhari da ƴan Najeriya ke ta kokawa a akai.
Ka da Tinubu ya kuskura ya dogara da wata yarjejeniya – Chief Chekwas Okorie
Wani tsohon ɗan takarar shugaban Kasa Chief Chekwas Okorie, ya ce wannan yarjejeniya ta Tinubu ba zai yi tasiri ba tunda ba dokar kasa bace.
” Can ta matse musu da yarjejeniyar su, mu dai abin da muka sani shine duk mai son yin takarar shugaban Kasa zai nemeta ne. Shima zai nema ne kamar kowani dan kasar nan zai yi.