Zargi: Wani sako a whatsapp na zargin cewa wata kasaitaciyar tawaga ta raka jagoran masu ra’ayin ‘yan awaren yarbawa Sunday Igboho zuwa kotu a jamhuriyar Benin.
‘Yan Najeriya sun zaku su san abin da ke faruwa da Sunday Adeniyi Adeyemo (wanda aka fi sani da Sunday Igboho) tun bayan da mahukuntan jamhuriyar Benin suka kama shi ranar 20 ga watan Yulin 2021.
Sunday Igboho, mai ra’ayin ‘yan aware kuma mai fafutukan kare hakkin kabilar yarbawa ya dade yana kira da a girka kasa mai zaman kanta (a bata suna jamhuriyar Oduduwa) wa kabilar yarbawa wadanda su ne mafi yawa a yankin kudu maso yammacin kasar. Shi dai Sunday Igboho yana da kasa biyu ne, wato yana da izinin zama dan kasa a Najeriya da Jamus.
Gwamnatin Najeriya tana mi shi kallon mai adawa da ikon halatacciyar gwamnati dan haka ta sa a kama shi. Sai dai Igbohon ya tsere lokacin da aka kai samame gidan shi ranar alhamis 1 ga watan Yulin 2021. Tun lokacin ya ke buya amma an cigaba da samun labaran karya dangane da kama shi har sai sadda mahukuntan Jamhuriyar Benin suka cafke shi a tashar jirgin saman kasar wato Cardinal Bernadin yayin da yake kokarin tserewa zuwa Jamus.
Kafofin yada labarai na gargajiya da na yanar gizo a Najeriya na cike da sharhunan jama’a dangane da abin da ya kamata ya faru da Igboho, yadda ya kamata a yi da shi a kurkuku da ma irin rawar da ya kamata mahukuntan Benin, da na Jamus da shugabannin yarbawa su taka wajen dawo da shi gida Najeriya, ko kuma sako shi da ma fafutukan da yake yi.
Wani bidiyo mai tsawon sakan 29 ya yi ta yawo a whatsapp a Najeriya in da aka nuno Igboho a cikin wata tawagar da ke biye da dimbin magoya baya suna karrama shi. Akwai wani rubutu a kan bidiyon da ke cewa “ZAKIN AFIRKA SUNDAY IGBOHO A KAN HANYAN SHI NA ZUWA KOTU A KWATANO”
Babu shakka Sunday Igboho ya kasance a kotu a jamhuriyar Benin, amma babu wani rahoto mai sahihanci dangane da tawaga ko ayarin motocin da ya raka shi zuwa kotu.
DUBAWA ta yi binciken mahimman kalmomi, inda ta gano bidiyoyi biyu masu tsawo amma ba’a yi musu rubutu ba. Bidiyon farko na da tsawon minti 9 da sakan 58, kuma ya kasasnce a shafin FaceTV Africa na YouTube. Bidiyon na dauke da sharhunan da ke yabon shi daga masu amfani da harshen yarbanci. Ranar 6 ga watan Yunin 2021 aka wallafa hoton da kwatance kamar haka: GA DIMBIN JAMA’AR DA SUKA MARABCI CHIEF SUNDAY IGBOHO A BABBAN JERIN GWANON ‘YAN KABILAR ODUDUWA.” Mutane sun kalli bidiyon har sai 1,303.
Bidiyon na biyu kuma na da tsawon minti 10 da sakan 2. Shi kuma an wallafa shi ne a shafin Gbefila TV amma bidiyon iri daya ne da wanda aka sanya a FaceTV Africa da taken GA DIMBIN JAMA’AR DA SUKA MARABCI CHIEF SUNDAY IGBOHO A BABBAN JERIN GWANON ‘YAN KABILAR ODUDUWA.” Mutane sun kalli wannan bidiyon sau 630.
Dubawa ta sake samun wasu hotunan bidiyon daga shafin yahoo wadanda suka nuna jerin gwano daban-daban da Mr. Igbohon ya yi a yankin kudu maso yammacin Najeriya kafin a kama shi amma bamu ga komai bayan da aka kama shi a Jamhuriyar Benin ba.
A karshe
Rubutun da aka yi kan gajeren bidiyon da ke zargin cewa Sunday Igboho ya je kotu a Kwatano da tawaga ba gaskiya bane. An gutsuro bidiyon ne daga jerin gwanon da ya yi a jihar Ekitin Najeriya a watan Yunin 2021.