SHUGABANCIN NAJERIYA A 2023: Tsarin karɓa-karɓa ba ya cikin tsarin mulki – Yahaya Bello

0

Gwamnan Jihar Kogi ya yi fatali da tsarin karɓa-karɓa, ya na mai cewa ba ya cikin ƙa’idoji, sharuɗɗa da hukunce-hukunce na kundin tsarin mulkin. Don haka a bar ‘yan Najeriya kawai su zaɓi wanda ya fi cancanta.

Bello ya yi wannan bayani ne a Abuja ranar Juma’a, a wurin taron masu aika rahotannin siyasa da laifuka.

Taron dai shi ne irin sa na farko, kuma sunan Yahaya Bello ɗin aka sa masa.

Gwamna Bello dai ya nuna maitar sa ta neman shugabanci a fili. Kuma tuni ake ta yi masa kamfen a ɓangarorin matasa na ƙasar nan daga ko’ina.

Ya ce a yanzu kamata ya yi a ce wanda ya cancanci shugabancin ƙasar nan, shi sai wanda zai iya haɗe kan ƙasar nan, ya dinke ɓarakar da ke ci gaba da yagewa kuma ya magance gagarimar matsalar tsaron ƙasar nan.

Ya ce to idan ma har karɓa-karɓa ɗin za a yi, ai yankin su na Arewa ta Tsakiya (Middle Belt) da Kudu maso Gabas ba su taɓa yin shugabanci ba tun bayan dawo da mulkin farar hula a 1999.

“Da tsarin karɓa-karɓa zai iya magance matsalolin tsaron Nijeriya, to da waɗanda su ka yi mulki aka tsayar da su da alfarmar karɓa-karɓa sun magance matsalar da yankunan da su ka wakilta ke ciki.

“Idan dai dimokraɗiyya za a bi, to kada a hana kowace jam’iyya tsayar da ɗan kowane yanki.

“Idan kuma karɓa-karɓa za a yi, to a yi bisa tsari na adalci da gaskiya. Domin Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas ba su yi mulki ba tun 1999.”

Yahaya Bello ya hori matasa su tashi tsaye su shiga gaba wajen hidimtawa a ƙasar nan, kamar yadda matasan sauran ƙasashen da su ka ci gaba su ka zabura wajen kawo wa ƙasashen su ci gaba.

Share.

game da Author