Shehu Sani ya fice daga PRP

0

Tsohon sanatan da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa daga 2015 zuwa 2019, Sanata Shehu Sani ya fice daga jam’iyyar PRP.

A wasikar da ya rubuta wa jma’iyyar kuma ya mika wa ofishinta dake mazabar sa, sanata Sani ya ce auren ta su ya kare daga yanzu sai dai za su ci gaba da zaman mutunci da irin zumunta ta gwagwarmaya da aka san jama’iyyar da ita.

Idan ba a manta ba sanata Shehu Sani ya fice daga APC shekara 2018, wato gab da zaben 2019, a lokacin da jam’iyyar APC ta musanya shi da Sanatan dake kan kujeran yanzu, Sanata Uba Sani.

Bayan musanya shi da jam’iyyar ta yi shine ya koma jam’iyyar PRP kuma yayi takarar wannan kujera ta sanata a wannan jam’iyyar sai dai bai yi nasara ba.

Sai dai kuma sanatan bai ayyana ko wacce jam’iyya zai koma ba.

Share.

game da Author