Sarkin Kano Aminu Ado yayi hatsarin mota a Kano, direba daya ya ji rauni

0

Kakakin rundunar Ƴan sandan Kano Abdullahi Kiyawa ya sanar da hatsarin mota da sarkin Kano Aminu Ado Bayero yayi a cikin garin Kano.

Haruna-Kiyawa ya bayyana cewa ” Daya daga cikin motocin dake tare da Sarki Aminu ne ya gogi wata mota kirar Toyota a Gadar Lado. Nan take ya garzaya da direban motan zuwa asibitin Murtala domin a duba shi.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta karyata labaran da ake yadawa wai an kai wa sarki Aminu hari don a kashe shi ne.

Share.

game da Author