Saraki ya shiga hannu, EFCC na tuhumar sa a Abuja

0

A yau Asabar ne hukumar EFCC suka cafke tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki domin tuhumar sa akan harkallar wasu kuɗaɗe masu yawan gaske.

EFCC na tuhumar Saraki ne kan wasu biliyoyin nairori da aka wabcewa daga asusun gwamnatin jihar Kwara a lokacin da yake gwamnan jihar ana karkatar dasu zuwa wasu asusun karya waɗanda mallakin Saraki ne a ɓoye.

PREMIUM TIMES ta gano cewa akwai wasu kamfanoni da asusun bad-da-kama da Saraki ya rika amfani da su ana jibga masa kuɗaɗe a ciki shi kuma yana ɗiba ya na shagalin sa da su, wanda kuma kuɗaɗe ne na jama’a a lokacin yana gwamna.

Waɗannan kudade sun zarce tunanin mutum domin kuɗaɗe ne da ake wabtar su ana waskewa da su ana danƙarasu cikin wasu ɓoyayyun asusu, shi kuma ya na kwasa yana shagalin sa da su.

Share.

game da Author