SAKI: Ba kaina farau ba, Allah ya isa tsakani na da masu zagi na – Mansurah Isah

0

Fitacciyar yar wasan finafinan Hausa kuma tsohuwar matan jarumi Sani Danja Mansurah Isah ta yi Allah-Wadai da irin kalaman da mutane suke yi mata na suka kawai wai don ta fita daga gidan Sani Danja.

Mansurah ta ce ba kanta farau ba.

Tun bayan rabuwar Mansurah da Danja mutane musamman a farfajiyar Kannywood ke ta tofa albarkacin bakunan su kan rabuwar, sai dai cikin su biyun babu wanda ya fito ya faɗi ainihin  abin da ya haɗa su.

A karon farko jarumar ta fito ta kuma maida wa waɗanda ke sukar ta martani cewa maganganun da suke yi akanta ya ya isa haka domin ba a kanta aka fara yin saki ba.

” Hmm. Nayi hoton Sallah, kunce abinda yasa na fito kenan, nayi tafiya zuwa wani gari kunce shi yasa na kashe aurena, naje cin abinci da kawayena, kunce iskancin da nake son yi kenan, naje aikin NGO na rabo dana saba yi yau shekara wajen 20 kenan ina yi, kunce daman yawon daya fito dani kenan.

” Yanzu wasu zasu ce Mansura kada ki kula su, ban damu da kowa ba, amma ku sani cewa rayuwata ce, zan yi duk abinda nake so da rayuwata, shin menene sabon abu a nan? Shin kalmar SAKI ce baku taba ji ba, ko kuma baku taba ganin mace da aka saka ba?

” Annabin Tsira (SAW) ya taba sakin mace. Allah daya halicce mu ya halarta. Mai kuke so a matsayin mu na muminai da bin dokokin Allah? Umarnin ku za a bi ko na Allah? Ni dai na san ban yiwa kowa laifi ba, wasu harda bude sabon shafin sadarwa don su zage ni.

” Haka nan kawai, ba ni kadai bace mace mai aure ko wacce aka saka a Social Media ba, in kunga yaran masu kudi tsirara ba dankwali a kan su, ko suna abindaa suka ga dama a social media, ku yabe su, in ‘yar fim tayi abu irin nasu, sai ku zage ta. Kun yiwa kan ku adalci?

” Kuji tsoron Allah, yara hadda ma tsofaffi fa, suna bina suna zagina. Idan kun koma gida ku tambayi iyayenku mata da ‘yan uwanku mata ko makotanku da aka taba saka yadda abin yake, ku tambayesu irin bakin cikin da suke ji. Ku ji amsar da zasu baku sai ku san irin illar da kuka yi mini. Ba zan taba yafewa duk wanda ya shiga rayuwata ba, Allah ya isa. Allah ya saka min, Allah abinda suke yi mini kayi musu, ka yiwa yaran su, iyayen su, ‘yan uwansu. Allah ka jarabce su da kuncin rayuwa na aure domin su gane kuskuren su. Ameen ya Allah. Amin dan wata mai albarka da muke ciki” inji Mansura Isah

Share.

game da Author