An kaure da hayani a majalisar Dattawa ranar Alhamis a dalilin rashin amincewar wasu daga cikin ‘yan majalisan kan a rika bayyana sakamakon zabe ta yanar gizo.
Bukatar hakan na kunshe ne a sabuwar dokar hukumar zabe dake gaban sanatocin suna tattaunawa da amincewa da da kodirorin don su zama doka.
‘Yan majalisan sun kaure da hayaniya bayan wasu daga cikin sanatocin sun kin yarda a wannan sashe na a yardar wa hukumar zabe ta rika bayyana sakamakon zabe a yanar gizo.
Abin ya kai ga har sai da shugaban majalisar ya ce a yi kuri’a tsakanin masu so da wadanda ba su son haka.
Ko da ya tambaya masu so suce ‘Ay’ wadanda ba su so su ce ‘Nay’. wadanda ba su so ne suka fi kara, amma ya doka gudumar sa akan wadanda suke so ne suka yi nasara.
A karshe dai abin bai yiwu ba har sai da aka kora yan jarida waje domin su yi ganawar sirri don a samu matsaya daya.