Sabuwar Korona nau’in ‘Delta’ ta yaɗu zuwa kasashe 98 – In ji Hukumar WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga kasashen duniya da su mike tsaye wajen dakile yaduwar cutar korona musamman yanzu da sabuwar nau’in cutar mai suna ‘Delta’ ke ci gaba da yaduwa a kasashen duniya.

Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi wannan kira ranar Juma’a yana mai cewa duniya na cikin wani mawuyacin hali ganin yadda yaɗuwar sabuwar nau’in Korona ke ci gaba musamman a kasashen duniya.

“Zuwa yanzu sabuwar nau’in cutar ta yadu zuwa kasashe 98 a duniya.

Ghebreyesus ya ce wayar da kan mutane kan ci gaba da kiyaye dokokin Korona, inganta yin gwajin cutar, inganta wuraren killace wadanda suka kamu da cutar, tallafa wa kasashen dake tasowa da mataman dakile yaduwar cutar musamman maganin rigakafi.

” Muna kira ga shugabanin kasashen duniya da su inganta yin allurar rigakafin korona domin ganin kowace ƙasa ta yi wa akalla mutum kashi 10% rigakafin cutar a yanzu sannan nan da shekara mai zuwa a yi wa kashi 70% na mutanen kasar.

” Yin haka zai taimaka wajen ceto rayukan mutane da farfado da tattalin arziki.
Bayan haka shugaban fannin shirye-shiryen dakile yaduwar korona na WHO Maria Van Kerkhove ta bayyana cewa tun a farkon bayyanar korona kwayoyin cutar ke yin rikiɗa.

Maria ta ce zuwa yanzu cutar ta canja yanayi sau hudu wanda kowacce nau’in cutar aka sa wa sunan Alpha, Beta, Gama da Delta.

“Banda haka ita kanta nau’in cutar Delta na da wasu nau’ukan cututtuka dake karkashin ta wanda a yanzu mun yi kira ga kasashen duniya da su fara gudanar da bincike domin ganin ko wadannan nau’ukan sun bayyana a kasashen su.

Share.

game da Author