Sabo da siyan jarabawa da satar ansa ya sa ɗalibai suka faɗi jarabawar JAMB warwas a kasar nan, Daga Ɗan Mohamman

0

Jarabawar shiga jami’o’i JAMB na bana ya tina wa ɗalibai da dama asiri ganin yadda fiye da rabin waɗanda suka rubuta jarabawar suka faɗi jarabawar.

Da ya ke lalacewa da taɓarɓarewar ilimi a kasar nan ya kai intaha, ɗalibai ba su karatu sai dai su jira lokacin jarabawa, su biya kuɗi a yi musu.

Sai kaga ɗalibi ya ci jarabawa harvya baka tsoro amma kuma idan ya shiga jami’a yayi ta fama da karatu da kyar ya ke iya cin jarabawa, wasu kuma ma koran su a ke yi daga ƙarshe.

Yanzu sai da kawai ayi sha’ani, domin har da malamai da masu makarantu ake haɗa baki a shirya wa ɗalibai yadda za su ci jarabawa.

Idan jarabawar kammala babban sakandare ne, a nan ne ma ya fi muni. Domin kusan yanzu hatta yadda kake son sakamakon ka ya kasance haka ake yi maka. Iya kudinka, iya shagalinka.

Sai kuma gashi a wannan karon da aka tsaurara tsaro, ɗalibai ba su sha da daɗi ba.

Masu jiran satar ansa ba su samu ba. Bayan sakamako ya fito sai kuma aka fara cewa wai da gangar hukumar JAMB ɗin suka kasa ɗalibai.

Yara sun zama malalata ba su karatu, kullum suna rike da waya suna Soshiyal Midiya, basu Facebook basu WhatsApp. Sannan ga kuma kalle kalle, iyaye sun sa musu ido saboda a karshe su ne za su biya kudin satar amsar don ƴaƴan su su ci jarabawa.

Ni na ga wasu da na sani da dama, da irin haka sula ci jarabawa kuma suna manyan makarantu yanzu. Wasu kuma shekaru uku kenan ba su iya cin JAMB ba. Kullum sai yake hakora mun ci WAEC, amma yaro bai san yadda ya ci WAEC ɗin ba.

Yanzu ana ta koke koke akai wai an kada ɗalibai. Babu wanda aka kada su dai ɗaliban suka kada da Kansu.

Abin dubi a nan shine, idan za a fito a faɗa wa juna gaskiya a fito. Yanzu jarabawa ya zama abinda ya zama. Idan a makarantun kasarnan ne, idan yaro ya faɗi jarabawar shiga ajin gaba, sai mahaifinsa ya je makarantar ya ce ko a kai shi ajin gaba ko kuma ya cire ɗan sa daga makarantar. Idan aka ki, akwai dubbai wanda zasu yarda a kawo musu ɗan idan har za a biya masa kuɗin makaranta.

Tun daga nan yaro ya samu gatan da bazai amfanar da shi ba, haka za a yi ta siya masa jarabawa har aikin ma siya musu yanzu ake yi.

Kana gida ba a ganka ba ma za ka siya fom a cika maka a yi maka jarabawa, illa iyaka ka zo ka karbi sakamakon jarabawa kuma yadda ka ke so.

Sai aukin na yi digiri amma, tun daga sakandare siyar jarabawa kake yi. Idan suka samu aiki sai su yi ta fama, gaba ɗaya sune a aikin gwamnati, inda nan ne kawai za su yi tasiri tunda dama sai ka ga dama ne za ka zo aiki, kuma idan wata ya kare a biya ka dole, Kuɗin gwamnati.

Share.

game da Author