Ruwan Maganin Allurar AstraZeneca ba ya sa a kamu da COVID-19 – Binciken DUBAWA

0

Zargi: Wasu sakonnin da ake yadawa a social media na zargin cewa allurar rigakafin kamfanin AstraZeneca na baiwa jama’a cutar COVID-19 kuma watakila ma allurar ce sanadiyyar karuwar cutar a kasar Liberia.

Wani sabon nau’in COVID-19 ya bulla a kasar Liberia a dai-dai lokacin da adadin wadanda ke kamuwa da kwayar cutar ya kai kololuwa a kasar. Duk da cewa kwayar cutar ta saba rikida, nau’o’in da da ke da lahani sosai ne abun damuwa, kuma abin da ke janyo ra’ayoyi mabanbanta ke nan a social media. A yanzu haka dai jama’a na zargin cewa ana samun karuwar adadin wadanda ke dauke da kwayar cutar coronavirus a Liberiya ne saboda allurar AstraZenecar da ake wa ‘yan kasar.

Ranar asabar 19 ga watan Yunin 2021 wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani labari inda yake tambaya ko dai allurar ce ke hadassa yaduwar cutar.

A labarin wanda tuni an riga an goge, mai amfani da shafin ya yi tambaya ga masu bin shafin na shi kamar haka: “Mun kula da cewa tun da aka kawo allurar rigakafi yawan masu dauke da cutar ya karu?”

Samar da allurar rigakafin AstraZeneca

Daga farkon wannan shekarar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amice da AstraZeneca a matsayin allurar rigakafin COVID-19 din da jami’ar Oxford ta sarrafa kuma ta sanya allurar a jerin wadanda za’a iya amfani da su a matakin gaggawa, abin da ya kara fadada damar samun allurar a kasashe masu tasowa saboda matsakaicin farashin da yake da shi.

A wata sanarwar da ta fitar WHO ta ce amince da allurar kamar yadda kamfanonin AstraZeneca-SkBio (Jamhuriyar Korea) da Serum Institute ta Indiya suka sarrafa.

Wani binciken da cibiyar yaki da cututtukar Amirka ta gudanar ya ce kamfanin AstraZeneca ya hada kai da jami’ar Oxford domin ya taimaka wajen samar da allurar ga mutane da yawa ba tare da nuna banbanci ko wariya ba, a duk fadin duniya a lokacin annobar.

Liberiya ta sami allurai 96,000 na AstraZeneca ta hanyar COVAX wanda ke samarwa kasashe allurar, ranar 1 ga watan Afrilu inda ita ma ta bi sahun kasashe da dama wajen kaddamar da allurar yaki da cutar ta COVID-19.

Ministan lafiya Dr Wilhelmina Jallah ya kaddamar da allurar rigakafin a ofishin lafiyar kasar tare da shugabannin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, wakilan Birtaniya da jakadun Tarayyar Turai, wakilan kungiyoyin ci-gaba, ministocin kasa, shugabannin kwamitocin lafiya, ‘yan majalisa, manyan jami’an gwamnati da manema labarai.

Daga nan an kai alluran sassa 8 a yankunan Montserrado, Margibi, wadanda suka hada da asibitin sojoji na Number 14, da asibitocin JFK, da na Cathotic da na Redemption da na SOS.

Tantancewa: Shin Allurar AstraZeneca na yi sanyawa mutun COVID-19?

Ministan lafiyar Dr Wilhemina Jallah, yayin da yake magana da wannan dan jaridan ta wayar tarho ranar 23 ga watan Yuni 2021 ya yi watsi da wannan zargi. Dr. Jallah ya ce ma’aikatar lafiya ba ta da wannan labari ko hujjar da ta nuna cewa allurar rigakafi na iya sanyawa mutane cutar COVID-19.

A cewar WHO, an gwada allurar AstraZeneca a dakunan gwaje-gwaje na zamani, an kuma gwada su a dubban dakuna masu kima sosai a idon jama’a wadanda kuma WHO ta amince da su.

Haka nan kuma AstraZenecar ce dai ake amfani da ita a duk kasashen duniya har ma da kasashen Afirkan da suka hada da Ghana, Saliyo, Mali da Morocco.

Dubawa ba ta sami wata hujjar da ta nuna cewa AstraZeneca na iya baiwa mutane COVID-19 a wadannan kasashen ba.

Wani binciken da aka yi a Birtaniya, ya nuna cewa idan mutun ya karbi allura daya ta Pfizer BioNTech ko AstraZeneca zai iya rage yiwuwar kamuwa da cutar a gida da kashi hamsin cikin 100. Ko wannan binciken ma bai sami hujjar cewa AstraZeneca na iya janyo cutar coronavirus ba.

A takardar bayanai dangane da alakar allurar AstraZeneca da cutar thrombosis ko kuma daskarewar jini, wanda sashen kula da lafiya na gwamnatin Australia ya wallafa, shi ma babu hujjar cewa cutar na iya shiga jikin mutun ta allurar AstraZeneca.

Shin mutun zai iya kama cutar COVID-19 bayan ya karbi allurar rigakafin AstraZeneca?

Cibiyar yaki da cututtuka ta Amirka, CDC, ta ce bayan an karbi allurar rigakafin COVID-19, kwayar cutar ba za ta bayyana a jikin wanda ya karba allurar ba idan aka duba da gwajin da ke gano ko akwai kwayar cuta a cikin jinin mutun, wato viral test a turance. CDCn ta kuma kara da cewa cikin dukkan alluran da aka amince da su, babu wadda ke sanyawa mutun kwayar cutar. Hatta alluran da ke matakin gwaji, wadanda ba’a riga an gama tantance su ba, su ma babu hujjar cewa zasu iya sanya wa mutun kwayar cutar.

Ba’a cika samun mutanen da suka kamu da cutar bayan an yi musu rigakafi ba, sai dai ba abun mamaki bani a sami kasancewar hakan. CDC ta ce akwai kalilan daga cikin wadanda suka karbi allurar da za su iya kamuwa da cutar sai dai ba zasu ji zafin cutar kamar wadanda basu taba karbar allurar ba.

A Karshe

Bisa la’akari da hujjojin da aka samu daga kimiyya, zargin cewa allurar rigakafin AstraZeneca ce ke janyo karuwar cutar COVID-19 a Liberiya karya ne.

Share.

game da Author