Rundunar ƴan sandan Kano ta kama wasu maza biyar da suka yi lalata da wani matashi ta baya a Mandawari

0

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama wasu maza su biyar da suka yi lalata da wani matashi dan shekara 20 ta baya da karfin tsiya a jihar.

Kakakin rundunar Abdullahi Haruna-Kiyawa ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a a garin Kano.

Haruna-Kiyawa ya ce rundunar ta samu wannan labari ne bayan wata mata mazauniyar kwatas din Mandawari ta kawo kara a ofishin su.

Ya bayyana sunaye da shekarun waɗanda aka kama kamar haka, Ahmed Inuwa mai shekara 34, Nasiru Isyaku Mai shekara 48, Lawan Uba mai shekara 31, Auwalu Uba mai shekara 40 da Rabiu Sharu mai shekara 33.

“Yayin da jami’an tsaron ke gudanar da bincike mutanen sun tabbatar cewa sune suka yi wa wannan ɗan shekara 20 fyade ta baya da karfin tsiya.

“An kai matashin asibitin koyarwa na Muhammadu Abdullahi Wase sannan har an sallame shi da ga asibitin.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Sama’ila Shu’aibu-Dikko ya bada umurnin a ci gaba da bincike akai har sai an gano ayyukan da waɗannan mutane ke aikatawa na wanda ba tun yanzu ba.

Haruna-Kiyawa ya ce za a za a mika waɗannan mutane kotu da zaran an kammala bincike domin yanke musu hukunci.

Share.

game da Author