Ruf da cikin da masu mulki suke yi akan guraben aikin gwamnati, yana rusa ingancin aikin gwamnati da cusa ƴaƴan Talakawa a Tasko, Daga Ahmed Ilallah

0

“Kimanin Yan Nijeriya Miliyan 85, zasu rasa aiyukan su” Inji Ministan Kimiyya da Fasaha, Malam Mohammed Abdullahi.

Wai, yau a Nijeriya akwai hukumomin gwamnatin Dan-Talaka bai isa yayi aiki a ciki ba, ko da na gadi ne ko bayin filawa. Wai, yau a Nijeriya abin birgewa ne Sanata ko Minista ya sanya offer (takardar samun aiki) ko hoton mutanen da ya samawa a dandalin Sada Zumunta na Zamani (Social Media) aiki a gwamnatin kasar su. Yau takai makurar da duk matashin da kaga yana aiki a NNPC, CBN, FIRS, NIMASA da sauransu, to dan wani ne, ko da wani dalili yaje wannan wurin. Dan Talaka duk ilimin ka, ko fasahar ka, kuma duk burin taimakawa kasarka, sai dai kayi hakuri.

Wai, yau a Nijeriya duk kankantar aiki, indai na gwamnati ne, sai dai a kasa a faranti, jagororin siyasa su rabawa dangin su da yayansu da wanda suke kauna. Yau a Nijeriya ba a maganar chanchanta ko ilimi ko fasaha, a a waka sani, waya kawo ka.

Wai, yau a Nijeriaya hatta aiki rage radadi, da gwamnatin tarayya ta fito dashi, sai da aka kai ruwa rana, tsakanin masu madafan iko, dole sai an raba an ba kowa kason sa. Mu koma muyi nazari game da matasan 1000 da aka dauka a duk kananan hukumomin Nijeriya, don aikin shara, wayanda ake biya N20,000 (dubu ashirin) duk wata, munga jaturbar da akayi tsakanin bangarenzartarwa da masu doka na wannan kasar.

Ko daga ina matsalar take? A wannan zamanin da muke ciki, wanda yafi kowane zamani hatsari a tarihin Nijeriya tun bayan yakin basasa wato (Civil War), kullum sake dulmiya ake cikin matsaloli kala daban daban. Kamarin rashin tsaro, tafiyar chacchaka da tattalin arzikin wannan kasa da yake yi. Kai uwa uba ma, rashin ingancin ilimi, rashin ingancin kiwon lafiya da kuma yawaitar rashin aikin yi a tsakanin matasan mu.

Babban tashin hankalin shine karuwar rashin aikinyi ga matasan mu a ko wace rana. A jiya ma 26 ga wantan Yuli, Ministan Kimiya da Fasaha, Malam Mohammed Abdullahi , a wani taro na kaddamar da wani shiri (Generation Unlimited Nigeria) ya sake tabbatar da cewa, kimmanin Yan-Najeriya, miliyan 85 (miliyan tamanin da biyar) ne zasu rasa aiyukansu, saboda gibin ilimin sadawar na zamani.

Kusan yau a cigaban duniya, a kasarnan ne kawai wannan mummunar al’ada take da tasiri. Al’adar siyasantar da samawa al’umma aikin yi. A wannan zamanin, masu rike madafen iko, zabbabu da wanda aka nada su kan yi kamfeyin da jan hankalin al’umma, da sunan sama musu offer ta aikin gwamnati.

Wannan abin takaicin ya hada da Senatoci, membobi na house of representative, ministoci da masu rike da manyan ma aikatan gwamnati. Kusan babu kunya da kuma hangen gaba har tallata takardun suke ko samfotin matasan da aka dauka aiki suke a kafafen sadarwa na zamani.

In har shugabban baza su samar da yanayi na adalci ba, wajen samawa matasan su aiyukan yi, bisa ilimin su da fikirar su da kuma damar da suke da it aba, a wannan kasa, to tabbas akwai alamomin tasgaro da gazawa na jagororin siyasar wannan zamanin.

Kyakkyawan tunani da la’akari da yawan yan kasan nan da ya haura miliyan 200 (miliyan dari biyu) ta yaya kowa zai samu alaka da masu mulki, har su bashi aikin yi duk chanchantar sa, ko kwarewar sa da baiwarsa.

Kullum ingancin aikin gwamnati narkewa yakeyi duk da duniya ta haska wa kowace kasa layin ci gaba, da damammakin aiyukan yi, bisa bullowar cigaban fasahar sadarwa ta zamani.

Wannan mummnar ta’ada, ta kusa ta ja layi tsakanin yayan masu mulki da yayan talakawa, domin yau ilimi, kwarewa da baiwa bata samawa kowa aikin a ma’aikatu irin su NNPC, CBN, FIRS da makamantan su, yau a wannan ma’aikatu sai wane ko da wane, bama a sanin lokacin da suke daukar aiki, imma an tallata, to an rabar da guraben aikin (vacancy). Duk wanda yaje wurin, to akwai wanda ya turahi. Wannan yana daga cikin gazawar wannan hukomomin su fidda kasar nan da ga matsalar tattalin arziki.

Wai shin, lokaci baiyi ba, da zamu tambayi kanmu, mai yasa, har yanzu matsalar ilimi ta gagare mu? Mai yasa matsalar kiwon lafiya ya gagaremu ne? mai yasa kullum barazanar tsaro ke ta karuwa ne? duk wannan ya tallakane da gazawar hukumomin gwamnati ne don aiwatar da aiyukan su da kuma rashin adalchin shugabanni wajen sauke nauyin da ke kansu.

A yau ba a maganar zagulo, nagartattun mutane, masu hazaka da ilimi don basu aiyuka da jagoran a muhimman hukumomin kasar mu. Wannan ya saba da tunanin kasashe da suka ci gaba, wayanda har hayar kwararru suke daga wasu kasashen don ci gaban kasar su.

Amma fa hausawa sunce in ana ta barawo to abi ta mabi sayu, su mafa yan kasar, sun kasa banbance aiyukan shgabannin su, sunki suyi tunannin menene adalcin da shugaba zai yi musu, sun gaza zabawa kansu shugabanni masu nagarta, kai sun zamanto akalar da ake jan su, basu suke ja ba.

Wai a wane lokaci za a samu Nijeriayar da dan talaka zai samu walwala? A yaushe burin matasanmu zai cika na ilimi da fasaha don ci gaban kasarsu?

Tabbas matasan kasan nan, musamman ma yayan talakawa suna cikin tasku da rauwa mai wahala don rashin samu aiyukan yi

Share.

game da Author