RIBAR-ƘAFA KURA TA TAKA KWAƊO: ‘Yan sanda sun kama Sowore wurin kallon shari’ar Nnamdi Kanu, a Abuja

0

Ɗan taratsi kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama shi a harabar Babbar Kotun Tarayya ta Abuja.

An kama shi ne wurin ƙoƙarin ganin yadda shari’ar Nnamdi Kanu za ta kaya a yau Litinin a kotun.

Sowore da kan sa ne ya yaɗa bayanin damƙewar da ya ce ‘yan sanda sun yi masa, ta saƙon WhatsApp da ya riƙa aikata.

“Yan sanda sun kama Ni a harabar Babbar Kotun Tarayya, a Abuja, wajen shari’ar Nnamdi Kanu.

“Sun riƙa jijjibga ta, sannan su ka sungume ni zuwa Ofishin ‘Yan Sanda na Sakateriyar Gwamnatin Tarayya.” Haka Sowore ya watsa.

An kama shi a gaban jama’a da ‘yan jarida, waɗanda jami’an ‘yan sanda da na SSS su ka hana shiga ɗakin shari’ar.

Tun da farko a ranar Lahadi, an riƙa watsa wata wasiƙa wadda aka danganta da Hukumar SSS ta Ƙasa a Abuja.

A cikin wasiƙar, an bayyana cewa ‘yan jarida 10 ne kaɗai aka amince su shiga ɗakin shari’ar a yau Alhamis.

A cikin sanarwar, an rattaba sunayen ‘yan jaridar da jaridun da kowanen su ke wakilta, cikin su har da PREMIUM TIMES.

An kuma amince wakilan gidajen talbijin na NTA, Channels da TVC kowane ya je da mai kyamara na bidiyo guda ɗai-ɗai a kotun.

Sowore na ɗaya daga cikin masu taratsin a saki Nnamdi Kanu, tare da ƙarajin cewa ba a bi halastacciyar hanyar da diflomasiyya ta gindaya ba lokacin da za a kamo Kamu a dawo da shi Najeriya.

Share.

game da Author