Wasu daga cikin manyan Kwamitin Amintattun Ƙungiyar ‘Yan Najeriya mazauna Amurka (NIDO Americas), sun nesanta kan su da ƙungiyar daga wata wasiƙar da wasu ‘yan Najeriya mazauna Amurka su ka aika wa Shugaba Muhammadu Buhari, inda a ciki su ka zargi Gwamnatin Buhari da nuna fifiko, son kai da ɓangaranci a lamarin tafiyar da mulkin sa.
A cikin wasiƙar sun yi ƙorafi da kuma nuna damuwa dangane da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a ɓangarori daban-daban na ƙasar nan.
To sai dai kuma sun yi ƙorafin cewa wasu tashe-tashen hankulan su na faruwa ne saboda abin da su ka kira ɓangarancin da Gwamnatin Buhari ke nunawa da nuna fifikon da su ka ce gwamnatin ta na yi.
Cikin wasiƙar wadda aka rubuta a ranar 6 Ga Yuni, ta na ɗauke da nuna damuwa kan yadda gwamnatin Buhari ba ta maida hankali wajen kakkaɓe ‘yan ta’adda da masu garkuwa, kamar yadda take yawan kai wa masu iƙirarin neman kafa ‘Biafra’
Wasiƙar da aka aika wa Buhari ɗin dai ɗauke ta ke da sa hannun Eromonsele Idahosa, Yinka Tella, Moses Timta da kuma wasu mutum uku.
Sun ja hankalin Shugaba Buhari dangane ya yadda ake samun bayyanar masu fitowa su na nuna ɓallewa daga Najeriya a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Wasiƙar ta nuna damuwa yadda “ba a kwankwatsar Fulani ‘yan bindiga kamar yadda ake bin masu neman kafa Biafra ana kashewa da mirtsikewa ta hanyar kisan rubdugun da ƙungiyar ta ce ana yi masu a nan Najeriya.
Haka nan wasiƙa ta nemi a bijiro da wani Kundin Tsarin Mulki wanda bai tauye kowane ɓangare ba, kafin zaɓen 2023.
Sun ma bayar da shawarar yin amfani da Dokokin 1963 da kuma rahoton Taron Tattauna Tsarin Mulkin Najeriya da aka gudanar cikin 2914, a matsayin ginshiƙin sake wani kundin dokar.”
Sai dai kuma a tattaunawar su da wakilin PREMIUM TIMES a Washington DC, babban birnin Amurka, Obed Mogano da ƙungiyar NIDO a Jihar Ohio da Micheal Essien na NIDO da birnin Minnesota, sun yi watsi da wasiƙar tare da cewa ta buge ce, holoƙo ce kuma ta bogi ce.
Obed dai Shugaba ne shi kuma Essien Mashawsrci Kan Harkokin Shari’a ne na ƙungiyar.
“Waɗanda su ka aika da wasiƙar ‘yan daƙa-daƙa ne, kuma sun yi amfani da suna na su ka yi sojan-gona.”
Wannan ƙungiya dai ta na da rassa daban-daban a Nahiyoyin duniya. Akwai NIDO ‘Worldwide, NIDO Oceania, NIDO Asia, NIDO Europe da NIDO Afrika.
NIDO Americas ta ƙunshi NIDO USA, NIDO Americas Canada da sauran su.
“A ƙarƙashin dokar NIDO, tilas sai Kwamitin Amintattun Ƙungiyar kaɗai zai yi magana da jami’an gwamnatin Najeriya.
“Doka ta ce NIDO ta kowace ƙasa, a can ƙasar ce kawai za su magana kan wani lamari a cikin ƙasar.”
Sun kuma zargin cewa a waɗanda su ka rubuta takardar sojan-gona su ka yi na tambari da kan-sarkin da suka buga a kan wasiƙar.
Sai dai kuma Moses Timta da PREMIUM TIMES ta tuntuɓe shi, ya yi biris da zargin da su Essien su ka yi masa.
“Idan ma laifi ne ai mu ne za mu fito mu ɗauki alhakin aikatawa. Ballantana kuma ba mu aikata laifin komai ba, mun yi ne saboda kishin ƙasar mu.” Inji shi.