• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Buhari Travelling

    Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

    An cika sansani uku fal da tubabbun ‘yan Boko Haram -Gwamna Zulum

    An cika sansani uku fal da tubabbun ‘yan Boko Haram -Gwamna Zulum

    RUƊANI A APC: Gwamnan Neja, Bello ya ɗare kujerar Buni, Buhari ya bada umarnin Buni ya sauka daga shugabancin jam’iyyar

    IHU BAYAN HARIN SHIRORO: Gwamnatin Neja ta dakatar da haƙar ma’adinai a Shiroro, Munya da Rafi

    Barayi sun lalata tiransifoma 20 cikin makonni uku – Kamfanin Raba Wutar Lantarki

    Barayi sun lalata tiransifoma 20 cikin makonni uku – Kamfanin Raba Wutar Lantarki

    SADAKA GUZURIN KIYAMA: Tsohon gwamnan da ya taya akanta jidar naira biliyan 84, ya yi wa malamai da ‘yan APC watandar shanu 370, ragunan layya 3,500 a Zamfara

    SADAKA GUZURIN KIYAMA: Tsohon gwamnan da ya taya akanta jidar naira biliyan 84, ya yi wa malamai da ‘yan APC watandar shanu 370, ragunan layya 3,500 a Zamfara

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

    ZAƁEN GWAMNAN OSUN: Matsalar tsaro da guguwar sayen ƙuri’u ne abin da ya fi damun mu -INEC

    Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

    Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

    ‘Na sadaukar da rayuwa ta ga Najeriya’ – Inji sojan da mahara su ka kashe a harin Shiroro

    ‘Na sadaukar da rayuwa ta ga Najeriya’ – Inji sojan da mahara su ka kashe a harin Shiroro

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su kai wa sojoji da mobal farmaki

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

No Result
View All Result

RAHOTON MUSAMMAN: Yadda farashin kayan abinci ke gudun famfalaƙin tsere wa talaka

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
July 24, 2021
in Harkokin Kudade/Noma
0
NAJERIYA: Anya Jiya Tafi Yau Kuwa? Daga Abdulaziz Abdulaziz

Nigerian Market

Yayin da talakan Najeriya ke kwana da tashin mafarkin kullum za a samu sauƙin rayuwa a cikin halin rashin tsaro daga Boko Haram da ‘yan bindiga, shi kuma farashin kayan abinci sai cillpawa sama ya ke ƙara yi, ta yadda ko talakan ya tuma tsalle ba zai iya taɓo abincin ba.

A cikin shekarar nan bincike ya tabbatar da cewa farashin abinci mai gina jiki da wanda ake ci kawai don maganin yunwa, duk ya tashi da kashi 58% bisa 100% a shekarar da ta gabata.

A wannan shekarar ma farashin bai sauka ba, sai ma ƙara hauhawa da ya ke yi, daidai lokacin da ‘yan bindiga ke fakewa a gonaki su ka damƙe manoma domin karɓar kuɗin fansa a wasu yankunan Arewacin Najeriya.

Binciken tantance farashin kayan abinci da PREMIUM TIMES ta gudanar a wasu jihohi bakwai, ya tabbatar da tashin farashin duk wani kayan abinci mai rai da lafiyar gina jiki zuwa kashi 69.5% bisa 100%.

Shi ma farashin abincin da ake ci maganin yunwa da abincin ci-kar-ka-mutu, ya ƙaru da kashi 59% cikin 100%.

Wanann tsadar kayan abinci na nufin da mai ƙarfi da marasa ƙarfi a Najeriya sun koma kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen abincin da iyali za su ci.

Sannan kuma ya na nufin musamman yara ba su samun abincin da zai gina masu jikin da za su rayu su girma cikin ƙoshin lafiya.

Har yanzu dai Najeriya ba ta iya ciyar da kan ta da dukkan al’ummar cikin ta. Ana dogaro ne da shigo da abinci daga ƙasashen waje, domin cike gurbin wanda ke ƙaranci.

Tun daga kayan abinci mai gina jiki irin su kifi da kayan masarufi irin su sukari, da abincin da ake ci maganin yunwa irin su masara, duk ana shigo da su cikin ƙasar nan har yanzu.

Duk da maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a harkar noma, a cikin watan Yuni PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wani bincike da ya nuna hatta rogo ma ba a iya noma wadatacce a ƙasar nan, duk da cewa ko’ina ana amfani da shi, ta hanyar sarrafa shi a yi abinci iri daban-daban.

Rufe kan iyakokin ƙasar nan da Gwamnatin Buhari ta yi domin bunƙasa noman abinci a cikin gida, bai haifar da ɗa mai ido ba, sai ma nunkawa da farashin shinkafa ya yi a faɗin ƙasar.

Ɗaɗin daɗawa kuma matsalar rashin tsaro da ta kai manoma su na ƙaurace wa gonakin su, ya ƙara damalmala lissafin ƙara dulmiyar da talaka ke yi a cikin ƙuncin rayuwa.

Binciken PREMIUM TIMES kan farashin naman shanu, naman awaki da tumaki da naman kaji da kuma kifi da doya, garin kwaki, ƙwai da garin semovita sun nuna irin yadda lamarin ya shafi talaka a shekarar da ta gabata. Kuma a wannan shekarar ma sai abin da ya ƙaru.

Naman kaza kilo ɗaya da ake saye Naira 1300 zuwa koma Naira 1700, ya koma naira 1800 zuwa naira 2500.

Shi kuma kilo ɗaya na naman shanu na naira 1550, ya koma naira 2000.

Farashin babban buhun bisashen kifi ya tashi daga naira 40,000 ya nunka zuwa naira 80,000.

Har Yanzu Tsadar Rayuwa Na Wuju-wuju Da Marasa Galihu:

PREMIUM TIMES a cikin Yuli ta buga yadda har yanzu tsadar rayuwa na wuju-wuju da marasa ƙarfi a Najeriya – NBS

Tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da na masarufi na ci gaba da nukurkusar marasa ƙarfi a Najeriya, sai dai kuma kisan-mummuƙe ta ke yi, wato a hankula.

Ƙididdigar farashin kayan abinci da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta yi, ta nuna cewa farashin kayan abinci na ƙara tashi, shi ya sa ko da malejin ƙuncin rayuwa ya ragu, kamar yadda ya ragu zuwa kashi 17.75 a watan Yuni daga kashi 17.93 na watan Mayu, talaka ba zai ji wani canji ba.

Haka dai NBS ta bayyana a cikin rahoton ta a ranar Juma’a.

Ta ce farashin kaya da na ayyukan yau da kullum sun tashi kamar yadda Hukumar Kula da Farashin Kayayyaki (CPI) ya tabbatar a cikin watan Yuni, 2021, zuwa kashi 17.75.

Hakan ya nuna kenan an ɗan samu raguwa da ɗigo 0.18 daga ƙididdigar watan Mayu.

Lissafin dai ya na nufin farashi ya riƙa ƙaruwa a cikin watan Yuni, amma da kaɗan-kaɗan idan aka kwatanta da watan Mayu, 2021.” Inji NBS.

Ƙididdiga ta nuna farashin abinci ya tashi da kashi 21.93 cikin Yuni 2021 idan aka kwatanta da kashi 22.28 na cikin 2021.

Sanarwar ta ce kayan abincin da su ka haddasa tsadar sun haɗa da biredi, seralak, dankali, doya da madara da ƙwai da kifi, lemukan kwalba, man girki da nama.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda tun daga farkon wannan wata doya ta gagari mutanen Enugu, sun koma yi wa dankali cin hannu-baka-hannu-ƙwarya.

Wasu mazauna Enugu sun koma cin dankali ganin yadda farashin doya ya cilla sama, ya gagari nauyin aljihun su.

Wakilin NAN da ya karaɗe yawancin manyan kasuwannin Enugu a ranar Asabar da ta gabata, ya lura da cewa dankalin Turawa ya cika kusan dukkanin shagunan da ke sayar da doya.

Wasu masu sayar da doya mai tarin yawa, sun daina sayar da ita saboda tsada, sun koma sayar da dankali, domin yanzu shi ake saye, duk an ƙaurace wa doya.

Yayin da ake sayar da buhun dankali sukutum naira 7,000 zuwa naira 8,500, ita kuma saiwar doya 12 ana sayar da ita naira 6,400 har zuwa naira 7,000.

Yayin da ake sayar da tsaka-tsakiyar doya ɗaya naira 800, ana sayar da ɗan ƙaramin kwanon awo cike da dankali naira 200.

Wasu da aka tattauna da su, sun ce ai dankali ya yaye wa gidaje da dama ƙuncin rayuwa sakamakon tsadar doya.

Wani mai suna Uju Ufondu ya ce “aƙalla idan ka na da naira 500, za ka sayo dankali mai tarin yawa. Duk irin yadda aka sarrafa maka shi kuma za ku ci ku ƙoshi har ku sha ruwa.”

Ita kuwa Vivian Oba cewa ta yi ta dakatar da cin doya ta koma cin dankalin Turawa, saboda doya ta yi tsada. Dama kuma dankali ya fi doya sinadaran gina jiki.”

Wasu masu sayar da dankali sun shaida cewa farashin dankali ya yi arha sosai ne a yanzu saboda lokacin da ne. Ita kuwa doya lokacin ta ya wuce.

“Na daina sayar da doya, yanzu dankali na ke sayarwa. Saboda masu sayen doyar ce su ka daina, su ka koma sayen dankali.”

Ya ce idan bai koma sayar da doya ba, zai rasa kwastomomin sa kenan.

Kelvin Egwu da ke sayar da dankali cewa ya yi a kullum farashin doya tashi ya ke yi sama ya na ƙaruwa. “Shi ya sa na yi watsi da cinikin doya, na koma sayar da dankali. Har sai doya ta yi sauƙi kuma ta wadata sannan zan koma sayar da doya.” Inji Egwu.

Yadda Shan Jar Miya Ke Neman Gagarar Talaka Ko A mafarki:

Abubakar Isma’il malamin firamare ne a Kano. Shi kuma Opeyemi Adeyemi ma’aikacin wani kamfani ne a Obalende, cikin Legas. Su biyun kukan su iri ɗaya dangane da masifar tsadar rayuwar da ake ciki.

“A wannan matsanancin halin, wanda aka rage wa albashi sai ya yi murna kawai, tunda ba korar sa aka yi ba ɗungurugun.

“To ni ba kora ta aka yi ba, albashi na aka zaftare. Wannan ibtila’i da ya same ni, ya canja rayuwa ta da ta iyali na. Saboda a yanzu haka abincin rana gagara ta ya ke yi, sai dai na riƙa ‘yan kame-kame.

“Ko dai na ci gasasshiya ko dafaffiyar masara da rana, na kwankwaɗi ruwa, ko kuma na jiƙa gari da ruwa da sukari na sha, na saurari jiran abincin dare.” Inji Adeyemi, wanda ya ƙara da cewa:

“Kuɗin wutar lantarki na neman gagara ta. Sauƙi na ma ba ni da yara ƙanana da yawa, amma da sai kuɗin makarantar yara sun gagare ni biya.”

Kamar Adeyemi kamar Isma’il, malamin firamaren da ya ce, “ai ni rabo na da sayen ƙaramin buhun shinkafa tun kafin Buhari ya hau mulki.”

Malamin ya ce a yanzu kafin ka ga gidan talakan da ake yin abinci da jar miya, sai wane-da-wane. Saboda kayan miya sun yi tsada kamar wasu kayan alfarma.”

Isma’il ya ce ba ya iya sayen kwanon wake saboda yanzu ya kai naira 1,600. Masara da gero da dawa waɗanda talaka ne ke noma su, a yanzu ko sunan su talaka ya ji wallahi sai hankalin sa ya tashi.”

Matsalar da Adeyemi da Ismail su ka shiga, irin ta ce miliyoyin ‘yan Najeriya da dama ke ciki a halin yanzu.

Bincike ya nuna a kullum kayan masarufi da kayan abinci su na tashi. Abin da ake sayarwa a kasuwannin birnin, ba daidai farashin sa yake da kasuwannin ƙauyuka masu ci sati-sati ba.

“Abin damuwar a kullum shi ne yadda farashin ke tashi a kowace kasuwanni. Abin da ka sani naira 500, idan ka koma wani sati naira 700 za a ce maka.”

Dalilan Tsadar Rayuwa Ga Talakan Najeriya:

Ɓullar cutar korona a ranar 27 Ga Janairu, 2020: Hakan ya tsayar da komai a ƙasar nan, ya karya tattalin arziki, miliyoyin ‘yan Najeriya sun talauce yayin da aka ƙaƙaba kullen korona.

Ƙarfin Tattalin Arzikin Cikin Gida Ya Samu Tawaya: Saboda masana’antu sun daina aiki. Babu kayan da ake sassafawa a cikin gida ana fitarwa a waje.

Sannan kuma masu aiki a masana’antu sun tagayyara, saboda an tilasta masu zaman gida.

Tarzomar #EndSARS: Wannan tarzoma ta haifar da kashe-kashe da asarar dukiyoyi masu ɗimbin yawa.

Dakatar da kai abinci a jihohin kudu da aka yi na wani lokaci ya haddasa masifar tsadar kayan abinci a kudancin ƙasar nan.

Matsalar Tsaro: Wannan babbar matsala ta haddasa tsadar rayuwa a Arewa, domin yankuna da dama noma ya gagara. Sannan kuma wasu kasuwannin yankunan karkara sun daina ci. Dama a irin waɗannan kasuwanni ake samun amfanin gona da arha, ana kaiwa cikin birane da garuruwa ana sayarwa.

Ƙarshen makon da ya gabata PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda yadda buhun garin kwaki ya tsere wa talaka fintinkau.

Garin rogo, wanda a ƙasar Hausa aka fi sani da garin kwaki, ya na ɗaya daga cikin abincin da duk wanda a shekarun baya aka ga ya daddage ya na ƙasumar sa, to ana danganta shi da talauci ko ƙarancin wadatar aljihu ko ta abinci a gida.

Amma a yau, duk da ɗimbin kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke kashewa wajen bunƙasa noma, hakan bai hana garin kwaki fecewa a guje ba, ya bi sahun sauran kayan abincin da ake nomawa a gida wajen tsula tsadar tsiya.

Kamar yadda shinkafa, wake, masara, gero da dawa su ke neman su gagari talaka, tuni shi garin rogo ya shige gaban su wajen tsada. Ya tsere wa gero da dawa da masara. Kuma ya yi wa talaka fintinkau, sai gani sai hange daga nesa.

Buhun garin kwaki mai nauyin kilo 100, wanda a shekarun baya ake sayarwa naira 16,000, yanzu idan ba ka da naira 40,000 ba za ta ka iya sayen sa ba a jihohi irin su Cross River, inda ake ganin kamar can ne ma ya fi arha takyaf.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna dalilai da dama da su ka haddasa ko da talaka ya iya sayen garin kwaki domin ya ci, to ba zai iya yi masa cin a ci a ƙoshi ba, irin wanda a shekarun baya ake tasa taiba a gaba ana ci har ciki ya cika.

Miliyoyin ma’aikatan da su ka ƙunshi na gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi waɗanda albashin su bai kai naira 40,000 ba, ba su iya cin garin kwaki su ƙoshi su da iyalan su. Sai dai a yi cin daga-bana-sai-baɗi, wanda ake yi ranar da aka ɗauki albashi.

Maciya tuwon alabo, wanda ake yi da rogo, su ma yanzu sai gani sai hange, ba kowa ke iya buɗe ciki ya danƙari tuwon alabo ba, duk kuwa da sulɓin ta lomar tuwon ke da shi. Saboda ba ta da sulɓi a cikin aljihun talaka.

A Najeriya dai batun tsadar abinci kullum sai hauhawa ya ke yi, ya ƙi saukowa ko gsngarowa ko kuma mirginowa a ƙasa.

A ƙididdigar da Hukumar Ƙididigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa ta yi a watan Afrilu, ta nuna cewa cikin watan Maris, 2021 kayan abinci a Najeriya sun yi tsadar da ba su taɓa yi a tsawon shekaru huɗu da su ka gabata ba.

Garin kwaki wanda shi ne aka fi nomawa na biyu daga masara a ƙasar nan, a yanzu bincike ya nuna wanda ake nomawa ɗin ba ya wadata.

Manoma irin su Grace Ebit da wasu masana sun danganta matsalar da rashin nahartaccen tsari da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa, rashin kyakkyawan tsarin noma, rashin jari ko rashin lamuni daga gwamnati da kuma ƙarancin taki.

Masana sun ce kafin rogo ya sake yin arha a Najeriya, sai an dasa aƙalla metrik tan miliyan 28.3 a filin gonakin da aƙalla sun kai faɗin hekta miliyan 1.2.

Cikin watan Mayu PREMIUM TIMES HAUSA ta yi tsakuren yadda wake ya fi ƙarfin tukunyar girkin manoman da ke noma shi.

A ƙarshen watan Mayu PREMIUM TIMES Hausa ta buga yadda wake ke keman ya gagari talakan da ke noma shi.

Yayin da Hukumar Abinci ta Duniya (FAO) ta fitar da rahoton cewa farashin kayan abinci ya yi tashin-gwauron-zabi wanda bai taba yin irin tsadar ba tsawon shekaru 11, wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi, ya nuna cewa kayayyakin abincin da akasari talakawa ke ci domin rayuwar yau da kullum, su na neman su gagari talakawa.

Wake, masara, shinkafa da sauran kayan abinci sun tsawwala tsadar da ta kai yawancin magidanta sai dai su riƙa auno wanda za su iya ci a kullum. Saboda ba kowa ke da sukunin iya sayen kayan abincin da zai iya aniyewa ba.

Wakilin mu ya fara da farashin wake a cikin Kano, inda kwano ɗaya ya kai naira 1,200. Magidanta da ba su iya aunar kwano ɗaya a rana ɗaya, sai dai a riƙa auno ƙaramin gwangwanin madarar ruwa a kan naira 80.

“Bara kamar yanzu har naira 500 na kan tuƙa mota na je kasuwar Ladin Makole (Lord Macauley) na auno ko kwano nawa na ke so. Amma ka ga bana ko a can ya kai naira 1,000 ko ma ya haura.” Haka wani mai suna Alhaji Sani Mohammed ya shaida wa wakilin mu.

Wani mai suna Ali, mutumin Badume, cikin Karamar Hukumar Dawakin Tofa, ya tabbatar wa wakilin mu a ranar Larabar nan cewa, “a gaba na na ga ana sayar da babban kwanon awon ‘bangajin Sasakawa’ ɗaya na wake kan naira 1,500. To ka ga mu da ke noma waken nan a ƙauyukan mu, ba za mu iya cin sa yanzu haka da rani ba. Dama kuma ɗan wanda mu ke nomawa da damina, tun kafin kaka ta yi nisa mu ke cinye shi.”

Wani bincike da wakilin mu ya yi a Garki, cikin Jihar Jigawa, ya gano cewa a can ana sayar da wake kwano ɗaya naira 1,000. To sai dai kuma waken daraja-daraja ne, wani bai kai wani nagarta ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa ana sayen buhun niƙaƙƙen garin masara buhu ɗaya har naira 26,000 mai cin kwano 40.

Haka kuma a Kano akwai shinkafar waje, wadda aka hana shigo da ita, amma ana sayar da buhun ta mai cin kwano 17 da rabi, naira 25,000. Shi kuma buhun shinkafar gida, wadda ake kira mai tsakuwa naira 22,000.

Wani bincike da wakilin mu ya yi, ya fahimci yawancin gidajen marasa galihu da ke cin shinkafa da wake da mai da yaji, a yanzu haka ya gagara.

Da yawan gidaje an koma cin ɗanwaken fulawa da rana, ko kuma a yi wainar fulawa ɗin, a bai wa yara su riƙa dangwalawa da mai da yaji, madadin abincin rana.

Gidaje da yawa an daina ɗora girkin abincin dare. “Abin da wasu da dama ke yi, idan aka dafa na rana, to ba a ci a ƙoshi har a yi ‘hani’an’. Sai dai a ɗan ci a bi shi da ruwa, a rage sauran da za a ci da dare.

“Saboda ka ga dai ga tsadar abinci, ga kuma tsadar gas. To yawancin gidaje da gawayi su ke girki. Kuma aiki ne mai wahala. Sai su haɗa abincin rana da na daren duk da rana. Amma dai maganar gaskiya ba wai ƙoshi fa ake yi ba.” Inji wata mai fama da yara ƙanana a gaban ta, wadda ta ce wa wakilin mu kullum sai ta fita ta nemo kuɗin da za a yi abincin gobe.

“Wallahi ko a cikin 1984, lokacin mulkin Buhari na soja, da aka shiga masifar tsadar rayuwa, kayan abinci sun yi tsadar da har kwanon wake ya kai naira 9. Na san mutane da yawa a ƙauyen mu da su ka kasa sayen wake su shuka. Saboda kuɗaɗen su duk sun salwanta wajen ruguguwar canjin sabbin kuɗi a lokacin. Inji Malam Auwalu.

Tags: AbujaHausaLabaraiNajeriyaPREMIUM TIMES
Previous Post

Gazawar Buhari ya sa na canja wa ƴa ta suna daga Buhariyya zuwa Kauthar – Yahuza Jibia

Next Post

Ƴan bindiga sun yi wa hedikwatar ƴan sanda dirar-mikiya, sun jikkata jami’ai uku

Next Post
Yadda Mahara suka kashe mutum 9 suka sace shanu 500 a Sabuwa, jihar Katsina – Honarabul Danjuma

Ƴan bindiga sun yi wa hedikwatar ƴan sanda dirar-mikiya, sun jikkata jami'ai uku

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • KOWA TA SA TA FISSHE SHI: Ƙoƙarin haɗewar LP da NNPP ya kakare, Peter Obi zai bayyana mataimakin takarar sa ranar Juma’a
  • ‘Da gangar aka bari ƴan bindiga suka kai harin gidan yarin Kuje, saboda na yi ta faɗin hakan zai auku – Mamu
  • Ƴan bindiga sun babbake cibiyoyin kiwon lafiya sun yi dalilin dole aka rufe wasu 69 a Katsina
  • Dala ta ƙara kekketa wa naira rigar mutunci daidai lokacin tsadar kayan abinci
  • Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.