A ci gaba da tsiyaye wa da jam’iyyar PDP ta kaSSe ta yi, kakakin majalisar tarayya, Femi Gbajabiamila ya karanta wasikar sauya shekar ɗan majalisar.
Honarabul Jonathan ya ce ya gaji da rikice rikicen da ya cukuikuye PDP a dalilin haka ya shi dai yayi sallama da jam’iyyar kwata-kwata.
Wannan ribibin ficewa daga PDP da ƴaƴan ta su ke yi ya yi matukar yin tsanani yanzu domin kusan duk sati sai kaji wani dan majalisar Jiha, Tarayya ko Sanata ya koma APC. Bai tsaya ga ƴan majalisu ba kawai, harda shugabannin ƙananan hukumomi da tsoffin jiga-jigan jam’iyyar sun koma APC.
Masu fashin baki sun bayyana cewa wannan sauye-sauye da ƴan siyasa ke yi na da nasaba shirye-shiryen tunkarar zaben 2023.
Sai dai har yanzu ba aji wani jigo a siyasa ba ya koma PDP tukunnan ko suna jiran ta ɓare a APC ne bayan rudɗanin da za a samu a lokacin fidda ƴan takara su kwashe su buhu-buhu.
Sai dai kuma ita kanta PDP tana warwatse ne a cikin gida, suma har yanzu kansu ba haɗe yake ba. Wasu na a’a ne wasu na eh.
Sannan kuma baya ga zabukan da za ayi, kafinnan akwai matsalar rashin tsaro da ake fama da su a sassan kasar nan wanda shima gagarimar matsalace.