Dandazon matasa sun gudanar da zanga-zangar jin haushin kama gogarma Sunday Igboho da aka yi a Kwatano, Jamhuriyar Benin.
Matasan sun gudanar da zanga-zangar a Ibadan, a ranar Laraba.
Sun tashi daga ƙofar gidan Sunday Igboho ds ke cikin unguwar Soka, inda su ka karaɗe wasu manyan titinan Badun, su na rera waƙoƙin neman ‘yanci da kiran Gwamnantin Jamhuriyar Benin ta saki Igboho, kada ta miƙa shi ga mahukuntan Najeriya.
Mayan titinan da aka yi jerin-gwanon sun haɗa da Felele, Sanyo da titin Challenge.
Wakilin PREMIUM TIMES da ya shiga ya ga yadda zanga-zangar ta gudana, ya ga jami’an ‘yan sanda biye da su a gefe su na sa-ido domin ganin yadda zanga-zangar ke gudana.
Haka kuma wakilin mu ya ga jami’an farin kaya na SSS su ma su na sa-ido don kada zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tarzoma.
Waɗanda PREMIUM TIMES ta zanta da su, akwai Yusuf Ajikobi, Ayedokun Abiodun, Ajilo da kuma Azeez Suleiman.
Dukkan su sun nemi a saki Igboho, saboda a cewar su, mutum ne mai son zaman lafiya. Tashe-tashen hankulan da aka riƙa yi a yankin ne su ka kai shi bango, inji su.
Sunday Igboho ya faɗa hannun jami’an tsaron Kwatano bayan da ya tsallake farmakin ƙoƙarin kama shi da jami’an SSS su ka yi a gidan sa na Badun.
Har yanzu dai ya na can a tsare, ba a haƙiƙance za a maido shi Najeriya ba, ko kuma sakin sa za su yi.
Discussion about this post