Sanata Uba Sani dake wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa su irin nasu salon ba salon yin shela bane na duk wani abu da suka yi wa jama’a don neman suna.
Sanata Uba ya ce abubuwan da yake yi wa jama’ar yankin Kaduna ta tsakiya mutanen sune shaida amma shi nashi salon ba salon yin shela bane ga duk abinda ya ke yayi wa jama’ar sa.
Sanata Uba ya bayyana haka a hira da yayi da Talbijin din Arise a cikin wannan makon.
Da aka tambaye shi me yake yi game da tsaro da rashinsa ya addabi mutanen Kaduna musamman kananan hukumomin da ke karkashin gundumar da yake wakilta, wato Kaduna Ta tsakiya Sanata Uba ya ce lallai akwai abubuwa na taimako da yake yi wa mutanen gundumar sa.
” Ina tare da ‘yan uwa da mutanen yankin da nake wakilta a koda yaushe. Tambayar da kayi min cewa wai bana ziyartar su ko kuma bane zuwa garesu domin jin halin da suke ciki ba haka bane.
” Ni ba mutum bane da komai yayi sai ya tallata ko ya yi shela akai, wadanda na yi wa sun sani. Iyayen wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su duk muna tare a koda yaushe. Ko yau sai da muka yi waya da wasunsu. Mun taimakwa musu da sauran wadanda a wannan ibtila’i yake afka wa kuma gwamnatin Kaduna ta maida hankali wajen ganin an kawo karshen wadannan hare-hare.
” Ko a majalisa ina so aje a tambaya, za a gaya muku irin gudunmawar da nake badawa. Na kirkiro kudirori da dama wadanda suke gaban majalisa yanzu haka a na tattaunawa akai. Wasu daga ciki har an yi muhawara akai a karon farko.
Akarshe sanatan ya ce zai ci gaba da ba da yin aiki tukuru wajen ganin an kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar Kaduna. Sannan kuma ya jinjina wa gwamnan jihar Kaduna bisa kokarin da yake yi wajen ganin an kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.
Wasu da suka tattauna da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA a Kaduna sun shaida cewa sun gamsu da irin salon wakilcin Sanata Uba sani a majalisa da kuma yadda ya kula da al’umman mazabar sa.
” Duk da matsalolin da ake fama da shi na rashin tsaro, sanatan mu Uba Sani ya maida hankali wajen taimakwa wa irin wannan ibtilai ya afka wa. Akwai