Hukumar Samar da Irin Shuka ta Ƙasa (NASC), ta bayyana cewa Najeriya ta samar da irin shuka har metrik tan 100,000 a cikin shekarar 2020, wanda aka riƙa amfani da shi a nan cikin gida da kuma ƙasashen Afrika ta Yamma.
Babban Daraktan Hukumar NASC Dakta Phillip Ojo na ya bayyana haka, yayin ƙaddamar da Dokar Kare Tsirrai da Shuke-shuke ta 2021 PVP a ranar Alhamis a Legas.
An gabatar da Dokar Kare Haƙƙin Tsirrai da Shuke-shuke ta 2020 ɗin ga masu ruwa da tsaki, waɗanda su ka nemi a fara amfani da dokar gadan-gadan, ta yadda za a bunƙasa hada-hadar cinikin irin shuka tsakanin Najeriya da sauran ƙasashe.
Ya ce wasu kamfanoni 300 su ka samar da irin shuka ɗin, kuma nan gaba kaɗan yawan wanda ake sanarwar ɗin zai ruɓanya ko kuma su nunka sau uku.
Ya ce “Najeriya na samar da kashi 50 na irin shukar da ake shukawa a Afrika ta Yamma. Ƙasashen Afrika ta Yamma da dama na dogaro da Najeriya ne domin samun irin shukawa wadatacce.”
Ojo ya ce idan Najeriya na so kada a maida ƙasar nan jujin jibge tulin bolar irin shuka daga ƙasashen ƙetare, tilas ta kammala cika muradin ta na zama a sahun farkon ƙasashe masu cinikayyar irin shuka a faɗin duniya.
“Najeriya da Ghana su na bin juna ɗaya bayan ɗaya wajen ƙoƙarin su na ganin sun zama sabbin mambobin ƙungiyar UPOV domin su shiga cikin mambobin ƙungiyar irin su Kenya, Afrika ta Kudu, Morocco, Tunisiya da Tanzania, da sauran ƙasashen Afrikawa waɗanda tuni su ne daɗaɗɗun mambobin ƙungiyar ta UPOV.”
Sauran ƙasashen ƙungiyar sun haɗa da Chadi, Tsibirin Comoros, Congo, Cote d’Ivoire, Equatorial Guinea, Gabon, Guinea Bissau, Guinea, Mali, Mauritania, Jamhuriyar Nijar da kuma Togo.
Discussion about this post