Gogarman tsagerun Yarabawa Sunday Igboho ya yi iƙirarin cewa ya san inda ake sayar da bindigogi, don haka zai sayo ya raba wa wadanda ba su mallaki bindiga ba.
Ya faɗi haka ne a cikin wani bidiyo wanda ya faɗo hannun PREMIUM TIMES HAUSA, amma babu takamaiman ranar da ya yi kalaman.
Igboho ya yi kalaman a wata ganawa da ya yi da wani basaraken gargajiya, inda ya ƙara da cewa, “babu wata gwamnati da ta isa ta hana ni riƙe bindiga.”
“Na san inda ake sayar da muggan makamai, zan iya zuwa na sayo na raba wa yara na da sauran waɗanda ba su mallaki bindiga ba, domin kowa ya mallaka.”
Ya na magana dangane da kare kai gada harin da ya makiyaya ke kai masu.
A cikin bidiyon, Igboho ya nemi gudummawar kuɗi domin a sayo makamai a raba jama’a da dama su samu.
“Na san inda zan je na sawo na raba wa yara da ma waɗanda ba su da ita.
“Duk wanda jami’an tsaro su ka kama da bindiga, su ce ni Sunday Igboho ne ya ba shi.
PREMIUM TIMES ta kira kakakin sa Olayemi Koiki domin ya shaida mata rana da wurin da Igboho ya yi jawabin, amma bai ce komai ba.
Sai dai kuma duk da ɓaɓatu da cika-bakin da ya riƙa yi, Sunday Igboho ya ce a fita zanga-zanga Legas, amma shi ba zai samu damar halarta ba.
Igboho ya yi kira ga dandazon matasa su fita zanga-zangar neman kafa Ƙasar Yarabawa, wadda ya shirya yi a ranar a Asabar a Legas.
Cikin wata sanarwa da kakakin yaɗa labaran sa Olayemi Koiki ya fitar, Sunday Igboho ya ce barazanar Rundunar ‘Yan Sandan Legas ba za ta hana su fitowa ba.
“Za mu fito ranar Asabar. A ranar za mu ga shin su wa ke da Legas? ‘Yan sanda ke da Legas ko al’umma ko kuma Sanwo-Olu?
Sai dai kuma wani abu bambarakwai shi ne Igboho ya ce kowa ya fita, amma shi ba zai samu damar halarta ba.
Idan ba a manta ba, jami’an SSS na neman sa ruwa a jallo, tun bayan harin da su ka kai gidan sa a ranar Laraba da dare, ya tsallake ya arce.
PREMIUM TIMES ta buga gargaɗin ‘yan sandan jihar Legas, inda su ka ce duk wanda su ka kama a zanga-zangar gogarma Sunday Igboho sai mun jijjibge shi.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta bayyana cewa kada Sunday Igboho ya kuskura ko ɓatan-hanya ya kai shi Legas da sunan zanga-zanga a ranar 3 Ga Yuli.
Gogarmar neman kafa Ƙasar Yarabawa (Yoruba Nation), Sunday Igboho ya bayyana shirya zanga-zanga a Legas, ranar Asabar, 3 Ga Yuli.
Sanarwar da su Igboho su ka fitar ta ce za su yi zanga-zangar kuma babu wanda ya isa ya hana su.
“Mu na sanar da Gwamna Sanwo-Olu cewa za mu zo Legas mu yi zanga-zangar lumana. Sanwo-Olu ne ke da wuƙa da nama a Legas. Don haka shi kaɗai za mu sanar wa zuwan mu.”
Sai dai kuma Rundunar ‘Yan Sandan Legas ta ce duk mai son kan sa da arziki, kada ya kuskura ya fito zanga-zangar gogarma Igboho.
“Mu na da labarin Sunday Igboho zai shirya zanga-zanga. Shi da duk wani mai kunnen-ƙashi irin da, su sani duk wanda ya fito sai ya yaba wa aya zaƙi.”
Rundunar ta ce ta shirya tsaf domin daƙile duk wani tsagera, taƙadari ko maras jin shawarar na gaba da shi.
Dambarwar ta zo kwana bayan wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a gidan Sunday Igboho da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Discussion about this post