Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya ƙaddamar da buɗe wata makekiyar maƙabarta ta ‘yan kasuwa, wadda sai an biya maƙudan kuɗaɗe kafin a rufe gawa ciki.
Da ya ke jawabi wurin buɗe maƙabartar, Fayemi wanda Kwamishinar Muhalli ta Jihar Ekiti, Iyabo Fokunle, ya ce maƙabartar za ta iya ɗaukar gawarwaki 260,000.
Ya ƙara da cewa maƙabartar wani shiri ne na haɗin guiwa tsakanin Gwamnatin Ekiti da ‘yan kasuwa masu zuba jari.
Fayemi ya ce gina maƙabartar wani ƙoƙari ne daga gwamnatin sa na bunƙasa kasuwanci da zuba jari da aka bijiro da shi a jihar.
Ya ƙara da cewa duk da akwai hannun gwamnatin jiha a harkar kasuwancin, ‘yan kasuwa masu zaman kan su ne za su tafiyar da maƙabartar.
“Buɗe wannan makaranta zai magance barazanar gurɓata muhalli sanadiyyar rufe gawarwaki a gida da wasu ke yi.” Inji Fayemi.
“A Amurka da Birtaniya da ƙasashen Turai, ba a yarda a rufe gawar mamaci a cikin gidaje ba.”
A ƙarshe ya yi kira ga masu jari a cikin kasuwancin su ƙoƙarta su faɗaɗa harkar a cikin ƙananan hukumomi 16 na Jihar Ekiti.
Ya kuma roƙi ‘yan asalin jihar Ekiti mazauna wasu garuruwa cewa idan iyayen su ko ‘yan’uwan su sun mutu, to ɗauko gawar daga can su kawo su rufe a Ekiti, domin a bunƙasa kasuwanci a jihar, musamman tunda farashin rufe gawa a Ekiti zai fi na Legas tsada.
Daya daga cikin daraktocin kamfanin, wanda kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Ekiti ne, Abiodun Aluko, ya ce an buɗe bangaren Musulmai daban da na Kiristoci.