MURNA TA KOMA CIKI: An dakatar da Blessing Okagbare daga ci gaba da yi wa Najeriya gudu a gasar Olimfik

0

Duk da yin nasarar shiga rukunin na kusa da na karshe da ta kai wanda ake sa ran za ta ciyo wa Najeriya gwal, azurfa ko tagulla, Blessing Okagbare, mahukunta sun dakatar da ita daga ci gaba da fafatawa a gasar.

Wannan dakatarwar ya daɗa jefa Najeriya ciki tashin hankali ganin kwanaki biyu kenan da aka dakatar da ƴan wasan kasar har 10 daga ci gaba da fafatawa a gasar ta Olimpik saboda faɗi gwajin jini da suka yi.

Mahukunta sun ce sakamakonngwajin da aka yiwa jinin Balessing ya nuna cewa akwai wasu kwayoyin wasu sinadarai da ka sha masu sa juriya a cikin ciki wanda kuma irin waɗannan abinsah ko magunguna annharamta su a gasar.

Sai dai kuma abin bakin ciki shine ita Blessing ta kai matakin fafatawa a na kusa da karshe wato ‘Semi Final’ a gudun 100 meters, ranar Alhamis.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda aka koro wasu yan wasa har 10 cikin ‘yan wasa 18 da Hukumar Tantancewa da Gwajin Jinin ‘Yan Wasan Olamfik ta ce ba su cancanci su shiga gasar ba.

Hukumar ta ce ba su cika sharuɗɗa adadin gwajin jinin da Doka ta 15 ta ce kowane ‘yan wasa na wasu kaɓantattun ƙasashe su cika.

Hukumar Gwaji ta AIU ta gindaya cewa Dokar Haramta Amfani da Kwayoyi Domin Ƙara Kuzari (Anti-Doping Obligations), wadda aka ƙirƙiro a cikin watan Janairu, 2019, ta na da haƙƙin tabbatar da cewa an bi ƙa’ida tilas ‘yan wasa sun gwaje-gwaje guda ukun da aka ce su yi kafin lokacin fara gasar Olamfik ta zo.

Share.

game da Author