Minista Lai Mohammed ya lailaya ƙarya, bai ɗauki nauyin kamfen ɗin mu ba -‘Yan Majalisar Dokokin Kwara

0

Ƴan Majalisar Dokin Jihar Kwara na APC su 21, sun ƙaryata iƙirarin da Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed ya yi, inda ya ce shi ya ɗauki nauyin biyan kuɗin kamfen ɗin su da kamfen ɗin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara.

Cikin wani taron manema labarai da su ka kira a ranar Lahadi a Ilorin, su 21 ɗin sun ce ƙarya Lai ya ke yi.

“Duk abin da mu ka kashe wajen kamfen da fosta da sauran hidindimun zabe, duk Gwamna ya ba mu, a lokacin shi ma ya na takara.

“Sai fa Hedkwatar APC ta Ƙasa da ta bai wa kowanen mu naira 500,000. Amma Minista Lai ko sisi bai ba kowa ba.

“To ina Lai ya ke da jama’a ko da a ƙaramar hukumar sa ta haihuwa da har za su amince masa su ɗauki maƙudan kuɗaɗen da ya ce ya tara ya bai wa gwamna domin kamfen?”

Kalaman Da Su Ka Jawo ‘Yan Majalisar Dokokin Kwara Watsa Wa Minista Lai Mohammed Kasa A Ido:

“Gwamnan Kwara ya ci amana ta bayan ni kaɗai na kashe masa dukkan kuɗaɗen da ya ci zaɓen 2019”

Dambarwa da karankatakaliyar rikici na ci gaba da ƙara muni tsakanin Gwamnan Kwara AbdulRazaq AbdulRahman da Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, shekaru biyu bayan sun yi taron dangin ‘O to ge’ sun ruguza gidan siyasar Bukola Saraki a jihar Kwara.

Lai Mohammed ya bayyana cewa shi ya ɗauki nauyin takarar da Gwamna AbdulRahman ya ci zaɓen 2019, amma kuma yanzu ya zo ya ci amanar sa.

Yadda Na Ɗauki Nauyin Takarar Gwamnan Kwara -Lai Mohammed

“Bari na faɗa maku, ba don ni ba da AbdulRahman bai ci kujerar Gwamnan Kwara ba. Ni kaɗai na tara masa dukkan kuɗaɗen da aka yi masa kamfen da waɗanda shi ma ya yi kamfen da su.

“Mutumin da ba shi da ko ranyo, ni na riƙa bin abokai na, abokan siyasa ta, abokan arziki, ‘yan siyasa da ‘yan uwa na kusa da na nesa ina tara kuɗaɗen da Gwamna AbdulRahman ya yi kamfen.

“Ina ƙalubalantar duk wani wanda ya ba shi ko ya tara masa kuɗi ko nawa ne, ya fito ya ƙaryata ni.

“Ni na biya kuɗaɗen da aka ejan-ejan na jam’iyya da shugabannin jam’iyya a matakai daban-daban domin su tattaro mana masu jefa ƙuri’a.

Gudummawar Babura 500 Na Bayar Da Motoci 20 Don AbdulRahman Ya Ci Zaɓen 2019 -Lai Mohammed

Minista Lai ya ce, “hatta babura 500 da motoci 20 waɗanda aka raba, duk ni na bayar da su.”

“Haka na bayar da kuɗin kamfen naira miliyan 100 ga Ɗan Majalisar Tarayya Tunji Ajuloopin, amma ya dagargaje naira miliyan 70, aka nema aka rasa, sai naira miliyan 30 kaɗai ya yi kamfen da su. Kuma zaɓen na sa ne ba nawa ba.”

Sai Da Aka Ce Min AbdulRahman Kara Da Kiyashi Ne -Lai Mohammed

Lai ya nuna rashin jin daɗin duk wannan ƙoƙarin da ya yi wa Gwamnan Kwara, amma kuma tun tafiya ba ta yi nisa ba, ya ci amana ta.

Ya ce tun farko da wasu masu kaifin tunani su ka ya tattago AbdulRahman Abdulrazaq, an ba shi shawara cewa ya rabu da shi, domin kara da kiyashi ne, amma bai karɓi shawarar ba.

Da ya koma kan batun ‘yan jam’iyya waɗanda ba a yi wa rajista ba kuwa, Lai ya ce Shugaban Riƙon Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ya tabbatar masa cewa kafin a yi gangamin jam’iyya na Jihar Kwara, sai an fara yin cikakken aikin rajistar ‘ya’yan jam’iyyar waɗanda ba a yi wa rajista ba.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga cikakkiyar salsalar rikicin na su wanda ya samo asali sanadiyyar ƙin sabunta rajistar ‘yan APC na Jihar Kwara magoya bayan Lai Mohammed da sauran ‘yan ɓangaren sa.

Jaridar ta bada cikakken labarin yadda gaggan da su ka ruguza gidan siyasar Bukola Saraki sun fara ƙwaƙule wa junan su idanu a Kwara.

Shekaru biyu tun ba a yi nisa da yin amfani da salon kamfen ɗin ‘O to ge’ aka ruguza gidan siyasar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, daga sama har ƙasa a Jihar Kwara, tun ba a yi nisa ba har gayyar ta watse, zaratan da su ka ga bayan Saraki sun juya su na yaƙar junan su da makaman da su ka yaƙi Saraki da su.

Gidan Siyasar Saraki dai ya kafu ne tun zamanin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa na zamanin Jamhuriya ta Biyu, Olusola Saraki, mahaifin Bukola da Gbemisola Saraki.

Bayan Bukola Saraki ya yi Gwamna shekaru takwas, ya ɗora Abdulfatah Ahmed, wanda ya yi shekaru huɗu na farko a ƙarƙashin PDP.

Bayan kafa nPDP, ya bi Saraki sun koma APC, inda a can ma ya sake lashe zaɓe ya shekara huɗu.

To sai dai kuma gangamin ‘O to ge’ a lokacin zaɓen 2019 da aka yi domin kawo ƙarshen siyasar gidan Saraki, ya yi nasara.

Nasarar farko dai wanda APC ta tsaida takarar gwamna a Kwara shi ya yi nasara, wato AbdulRahman Abdulrazaq.

Nasara ta biyu kuma Saraki da duk waɗanda su ka fito takara a ƙarƙashin tutar sa sun ci ƙasa ba su yi nasara ba.

Gungun Ruguza Gidan Siyasar Saraki:

Wannan gungu sun haɗa da ‘Legacy Group’, wanda ya ƙunshi Gbemisola Saraki, ƙanwar Bukola Saraki, wadda ba su ga-maciji. Ita ce bayan nasarar zaɓen 2019 aka naɗa ta Ƙaramar Ministar Sufuri.

Akwai kuma gungun AA Group, wato Gwamna a yanzu wanda shi gungun mayaƙan su ka tsayar takarar gwamna, kuma ya yi nasara.

Akwai irin su Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, wasu ɗaiɗaiku irin shugaban jam’iyyar a APC na lokacin, Bashir Bolarinwa.

Yadda Aka Fara Kitso Da Kwarkwata A Cikin Kai:

Tun a wurin zaɓen fidda gwani aka fara samun tangarɗa, inda a bisa kuskure aka soke ‘yan takara biyu, Salihu Mustapha da Mashood Mustapha.

Sai da ta kai uwar jam’iyyar APC ta ƙasa sun ba su haƙuri dangane da abin da aka yi masu. Duk da wasu na ganin cewa tuggu ne aka ƙulla masu, amma dai sun haƙura ba su kai ƙara ba.

Dawowa Rakiyar Gwamna Watanni Shida Bayan Zaɓe:

An shafe watanni shida kafin Gwamnan Kwara A.A ya naɗa kwamiahinoni. Hakan kuwa ya ɓata wa da dama gaggan APC na Kwara rai.

An samu saɓani da cukumurɗar tuggu da kutunguilar siyasa, har ta kai an tsige Shugaban Jam’iyya Bashir Bolarinwa. An yi zargin da hannun Gwamna aka kori Bolarinwa daga shugabancin APC a Kwara.

Shugaban Kwamitin Riƙon APC, Mai Mala-Buni ya naɗa Abdullahi Samari shugabancin rikon APC a Kwara bayan tsige Bolarinwa.

Tsige naɗa Borarinwa da naɗa Abdullahi Samari, ya fasa jam’iyyar APC gida biyu a Jihar Kwara. Akwai masu goyon bayan Gwamna, akwai kuma waɗanda ba su goyon bayan sa.

Rigimar Gwamna Da Minista Lai Mohammed:

Alaƙa ta yi tsami tsakanin Gwamna da Minista Lai Mohammed a lokacin sabunta rajistar ‘ya’yan jam’iyyar APC, inda Lai Mohammed ya ce “iya-shege” aka yi ba sabunta rajista ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda Gwamnan Kwara ya tashi da katinan rajistar ‘yan jam’iyya sama, ya bar Lai Mohammed ya na susar ƙeya.”

Minista Lai a lokacin ya kira taron manema labarai a garin su Oro, inda ya nemi a sake sabunta rajista a jihar Kwara, domin Gwamna ya kwashe katin rajista ya raba wa magoya bayan sa.

Lai ya yi zargin cewa ba a bi tsarin da jam’iyyar APC ta gindaya wajen sabunta rajista ba.

Wakilin mu ya tabbatar da wani zargi da Lai Mohammed ya yi, inda ya ce ba a yi amfani da littafin rajistar mambobi ba, sai aka yi amfani da fallayen takardu, waɗanda hatta shi kan sa gwamnan ma da mutanen sa duk a fallayen farar takarda aka yi rajistar sunayen su.

Tuni dai wannan gayya ta watse kowa ya kama gaban sa. Jama’a da dama na ganin idan Saraki ya sake yunƙurawa a zaɓen 2023, zai dawo da martabar gidan siyasar Saraki daram.

Share.

game da Author