Jami’an ‘yan sandan Zamfara sun kashe wani Kasurgumin dan bindiga da ya addabi mutanen zamfara a arangama da suka yi da gungun yan bindiga ranar Laraba.
Kakakin rundunar Mohammed Shehu ya sanar da haka ranar Alhamis a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Shehu ya ce hakan ya faru ne bayan maharan sun yi garkuwa da mutum 12 a jihar.
Ya ce jami’an tsaron sun yi arangamar da maharan ne a hanyar Gusau zuwa Sokoto a Dogon Karfe.
“Jami’an sun ceto mutum 11 daga cikin mutum 12 da aka yi garkuwa da su sannan sun kashe daya daga cikin maharan.
Shehu ya ce rundunar za ta ci gaba da farautar maharan domin ceto sauran mutanen da ke tsare a hannun maharan.
Jihar Zamfara na daga daga cikin jihohin Arewa dake fama da rashin tsaro a kasar nan.
Discussion about this post