Manoma a yankin Abuja sun koka kan rashin tsaro da farmakin makiyaya

0

Matsalar rashin tsaro ta fannonin daban-daban na ƙara kawo barazana ga samuwar wadataccen kayan abinci a ƙasar nan.

Manoma da dama a cikin ƙauyukan yankin Abuja da sauran yankunan Arewa da Kudu, su na kokawa da yadda aka hana su zuwa gonakin su, domin tsoron ko dai kada a yi garkuwa da mutum a biya kuɗin fansa kafin a karɓo shi, ko kuma makiyaya su kai wa manomi farmaki, su kashe shi.

“Matsalar tsaro ta gurgunta min noman dankalin Turawan da na ke yi a Kunsa” Inji Esonu Udeala.

Udeala mai shekaru 58 ya ce makiyaya sun kawo masa cikas a gona sosai, har ta kai a daminar bana bai samu damar yin shuka da wuri ba.

“Tilas dai da jira lokacin da kowa ya fito ya fara yin shuka, sannan Ni ma na je gona na yi shuka, tsoron kada Fulani makiyaya su tura shanun su a cikin gona ta.” Inji shi.

Manomin wanda ya shafe shekaru 13 ya na noma, ya ce a wannan daminar ta bana ban fara noma da wuri ba, kamar yadda na saba yi a shekarun baya ba. A bana sai 15 Ga Yuli. A daminar bara kuwa tun ranar 15 Ga Yuni na yi shuka.”

Wani mai suna Okafor da wakilin mu ya nemi ya kai shi gonar da ya ga inda gonar ta ke a Kuje, ya ce sai fa idan zai sa hannu a kan takardar yarjejeniyar cewa duk abin da ya faru da wakilin na mu, to babu ruwan shi.

Shi kuwa Udeala cewa ya yi, “ranar 2 Ga Disamba makiyaya sun shiga gonar su da shanu. Ƙoƙarin su hana a cinye mana amfanin gona ya nemi haifar da mummunan rikicin da tilas mu na ji, mu na gani muka ƙyale shanun su ka cinye mana amfanin gona ƙarƙaf.”

Ya ce tilas ya koma Jihar Nassarawa, inda ya karɓi aron wata gona mai faɗin hekta huɗu, kuma an kewaye da da shinge na waya, ya yi noma a can.

“Saboda rashin tsaro gonakin da ke kusa da gari sun yi tsada. Saboda manoma ba su iya zuwa gonakin da ke cikin daji. Idan za ka karɓi aron gona mai faɗin hekta ɗaya, tilas sai ka biya naira 50,000 idan har ka samu gonar kenan.

Daniel Ukafor wanda ya ƙi yarda ya kai wakilin mu a gonar sa, ya ce gonar ta na da faɗin hekta biyar, amma ƙiri-ƙiri ga gonar can a ƙauyen Gaube a yankin Kuje, amma ba zai iya zuwa ya yi noma ba. Don kada ya je a sungume shi a nausa daji da shi.

Shi kuwa Aderibigbe Isaac-Taiwo, wanda shi ne Shugaban Mazauna garin Pegi a ƙarƙashin Kuje, ya ce a yanzu an daina yi wa yankin FCT Abuja kirarin “Babban Kwandon Abincin Ciyar da Najeriya”, wato ‘Food Basket of The Nation.’ Saboda noma ya ragu sosai. Ka na zuwa gonar da ke noma damƙe ka masu garkuwa za su yi. Idan aka sayar da gonar da ka ke taƙama da ita ɗin, ba iya biyan kuɗin fansar ka kuɗin za su yi ba.”

Share.

game da Author