Majalisar Dokokin Zamfara ta bai wa Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu sa’o’i 48 ya bayyana a gaban ta, domin ya kare kan sa bisa tuhumar rashin ladabi da ƙin bin umarnin da ta ke yi masa.
Sun bada wannan wa’adin ne yayin zaman su na ranar Talata, a ƙarƙashin Kakakin Majalisar, Nasiru Magarya.
‘Yan Majalisar su na zargin sa da shirya gangamin taron siyasa a daidai lokacin da ake zaman jimamin kisan da mahara su ka yi wa jama’a, a ranar 10 Ga Yuli, a Ƙaramar Hukumar Maradun, mahaifar Gwamna Bello Matawalle.
Dambarwar na ƙara tsamari wata ɗaya bayan da Mataimakin Gwamna ya ƙi bin Gwamna da ‘Yan Majalisa canja sheƙa daga PDP zuwa APC, a ranar 29 Ga Yuni.
Cikin makon jiya Gwamna Matawalle ya ce ya fi ƙarfin ƙaramin ɗan-tsako kamar mataimakin sa ya shigar masa hanci.
A makon da ya wuce kuma, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Kotun Tarayya ta hana Majalisar Dokokin Zamfara tsige Mataimakin Gwamna.
Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta hana Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da Cif Jojin jihar yin duk wani yunƙuri, shiri ko aiwatar da tsige Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau.
Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya bayar da umarnin a cikin wani hukuncin da ya yanke a ranar Lirinin, mai lamba. FHC/ABJ/CS/650/2021, wands jam’iyyar PDP ta kai ƙara, ya hannun lauyan ta mai suna Ogwu Onoja.
A tsarin dokar Najeriya dai Cif Jojin Jiha na da ƙarfin ikon kafa kwamitin binciken wani zargin da ka iya fuskantar tsigewa ga gwamna ko mataimakin sa wanda Majalisar Dokokin Jiha su ka yi.
Amma Mai Shari’a ya umarci Majalisa da Cif Jojin Zamfara kowa ya dakata har sai kotun ta gama sauraren ƙarar da PDP ta shigar kuma kotun ta yanke hukunci tukunna.
Sannan kuma kotun ta hana Majalisar Dokokin Zamfara ɗaukar duk wani mataki kan mambobin majalisar waɗanda su ka ƙi bin Gwamna Matawalle zuwa cikin APC.
Kotu ta dage shari’ar zuwa ranar 23 Ga Yuli, kuma ta umarci a gaggauta sanar da ɓangarorin hukuncin da kotun ta yanke daga yau Litinin zuwa Juma’a.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labari a ranar Juma’a, inda Kotun Tarayya a Abuja ta ɗage ƙarar neman ƙwace kujerar Gwamnan Zamfara daga hannun Bello Matawalle.
Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ɗage sauraren ƙarar da aka shigar ana neman kotun ta ƙwace kujerar Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ta maida wa PDP, saboda ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Wasu mambobin PDP na Jihar Zamfara, Sani Ƙaura Ahmed da Abubakar Muhammad ne su ka shigar da ita.
A ranar 17 Ga Yuni su ka shigar da ƙarar, makonni biyu kafin ma Matawalle ya kai ga canja sheƙar.
Sun yi saurin kai ƙarar ce inda su ka ce a bisa doka, tunda Kotun Koli ce ta ba shi kujerar, haramun ne ya ɗauke ta kacokan ya koma cikin APC ya ci gaba da zama a kan ta.
A lokacin sun ce idan zai koma APC, to sai dai ya sauka. Matawalle dai ya koma APC a ranar 29 Ga Yuli.
Yayin da aka koma sauraren ƙara a ranar Juma’a, lauyan masu ƙara, Kanu Igabi ya cire wasu kusassari biyu a cikin buƙatun da ya nemi kotu ta biya wa waɗanda ya shigar da ƙarar a madadin su. Wato su ne inda ya ce kotu ta dakatar da Gwamna da Mataimakin sa komawa APC.
Lauyan ya yi hakan domin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu bai koma tare da gwamnan ba, shi kuma gwamnan ya rigaya ya koma. Kuma ba a saurari ƙarar ba har Matawalle ya koma.
Lauyan Matawalle, Mike Ozekhome bai yi wata jayayya ba, ya amince Igabi ya zare waɗannan buƙata biyu.
Yanzu buƙatar lauya Igabi ta koma neman kotu ta tsige Gwamna Matawalle kenan.
Mai Shari’a Inyang Ekwo ya soke buƙatun guda biyu, sannan ya ɗaya ƙarar zuwa ranar 29 Ga Satumba.
Discussion about this post