Ƙasa da makonni biyu bayan Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya yi iƙirarin cewa a gidan Ibilis ne kaɗai zai yi shakkun zuwa ya ciwo bashi don yi wa Najeriya aiki, Majalisar Dattawa ta amince Shugaba Muhammadu Buhari ya karɓo bashin naira tiriliyan 2 da biliyan 343.
Adadin kuɗin dai daidai su ke da dala biliyan 6.1 a lissafin canjin kudi farashin gwamnati, ba farashin ‘yan canji ba.
Dattawan sun amince a ciwo bashin ne bayan sun karɓi rahoton Kwamitin Lura da Basussikan Cikin Gida da na Waje.
A cikin watan Mayu ne dai Shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa wasiƙar roƙon su amince ya ciwon bashin na dala biliyan 6.1 (naira tiriliyan 2.343).
Shugaban Kwamitin Lura da Basussuka na Cikin Gida da na Waje, Sanata Clifford Ordia, ya ce tuni dama Majalisa ta amince a ciwo bashin naira tiriliyan 4.6, tun a cikin dokar Kasafin 2021.
Waɗannan naira tiriliyan 2.343 kuwa su ma za a dulmiya su ne a matsayin cike giɓin da aka samu a Kasafin 2021.
Ya ce batun bashin ba wani sabo ba ne, domin tun lokacin da Majalisar Dattawa za ta miƙa kasafin 2021 akwai batun ciwo bashin a ciki.
Cikin makon jiya ne Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bugi ƙirjin cewa “Banda gidan Iblis ba inda zan ji tsoron zuwa karɓo lamuni.”
Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ƙasashen Turai sun buɗe wa Najeriya ƙofar shiga karɓar lamuni.
A wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja, yayin da ya ke masu bayanin za a fara aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano a cikin watan Yuli ɗin nan, Ameachi ya bayyana cewa har yanzu akwai bashin da za a karɓo daga Standard Chartered Bank, wanda za a yi aikin titin jirgin ƙasa na wasu sassan ƙasar nan.
“Haka kuma akwai lamunin da ba a kai ga amsa ba tukunna daga China Exim Bank, wanda za a yi aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Kano.
“Sai kuma wani lamunin da aka yi niyyar ciwowa daga wani kamfani a China, domin titin jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri. Ba a kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar ba, sai kuma ƙasashen Turai su ka buɗe mana rumbun su na bayar da lamuni.
“Karbo lamuni don a yi aiki ba wani abu ba ne. A matsayi na na Kirista, gidan Ibilis ne kaɗai zan ji tsoron zuwa karɓo bashi.” Inji Amaechi ya ke shaida wa manema labarai a Abuja.
Ya zuwa ranar 31 Ga Maris dai ƙasar Chana kaɗai na bin Najeriya bashin dala biliyan 3.4, waɗanda aka ciwo sau 11 tun daga 2010 zuwa 2021.
PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito Minista Amaechi ya e an biya dala miliyan 218, somin-taɓin fara titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano.
Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana wa manema labarai cewa Gwamnatin Tarayya ta biya dala miliyan 218, matsayin somin-taɓin fara aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano.
Amaechi ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce tantagaryar adadin kuɗaɗen kwangilar dala biliyan 1.2 ne. Amma daga cikin an fara biyan dala miliyan 218, domin a fara aikin titin cikin wannan wata na Yuli da mu ke ciki.
Amaechi ya ce yanzu hankalin gwamnatin tarayya ya karkato a kan aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano, tunda an rigaya an kammala na titin Legas zuwa Ibadan.
“A yanzu abin da ya rage a biya kudin aikin su ne dala miliyan 900. Kuma nan da makonni kaɗan masu zuwa za a sake biyan dala miliyan 100.” Inji Amaechi wanda ya ce ya na sa ran zuwa ƙarshen wannan shekara za a yi ƙoƙari a biya dala miliyan 600.
Ya kuma yi magana kan sauran titinan da Gwamnatin Tarayya ta ƙudidi aniyar shimfiɗawa, kuma duk na jirgin ƙasa daga na Maiduguri da na Ibadan zuwa Kano, da na Legas zuwa Calabar.
Ya ƙara da cewa an fara biyan kuɗin somin-taɓin aikin titin jirgin ƙasa na Kano daga Kaduna daga cikin kasafin gwamnatin tarayya.
“Akwai kuma sauran kashin kuɗaɗen wanda China ce za ta biya, amma ba ta fara biyan ba tukunna.
“Kada ku tambaye ni inda Najeriya ta samu kuɗin da ta biya. Domin a matsayi na na Kirista, gidan Shaiɗan ne kaɗai ba zan iya zuwa neman bashi ba.” Inji Minista Amaechi.
Discussion about this post