Majalisa ta shirya kafa dokar hana INEC soke sakamakon zaɓen da aka tirsasa jami’in zaɓe ya bayyana sakamakon bogi

0

Idan dai Majalisar Dattawa ta sake yin wani zurfin tunani ta yi fatali da ƙudirin ba, to za su amince da ƙudirin dokar zaɓe wanda ya fifita jami’in bayyana sakamakon zaɓe a kan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, ita kan ta.

Hakan ya na nufin duk sakamakon da jami’in zaɓe ya bayyana, to INEC ba ta isa ta soke ba. Alƙalami ya bushe kenan.

Wato wani azargagi ne ‘yan siyasa su ka ƙalla, wanda zai ba su lasisin cin zaɓe ko da maguɗi, ko da tsiya, ko da tsinin-tsiya, ko da fizgen akwati ko amfani da ‘yan sara-suka ko bindiga su tilasta jami’in bayyana sakamakon zaɓe ya bayyana sakamakon da ba na gaskiya ba.

Bai wa jami’in zaɓe iko fiye da INEC ita kan ta, zai iya sa ‘yan siyasa tirsasa shi da lalama ko da tsiya ya faɗi sakamakon da ba na gaskiya ba. Idan ya bayyana kuma, shikenan babu abin da INEC za ta iya yi.

An sha fama da ƙorafe-ƙorafen sauya wasu dokokin zaɓen 2010, waɗanda INEC ke ta ƙoƙarin ganin ana hukunta masu maguɗin zaɓe.

Sai dai kuma bijiro da wannan ƙudiri wanda PREMIUM TIMES ta gano zai iya haifar da koma baya ga sabunta tsarin zaɓe da kuma cikas ne ga hoɓɓasan da INEC ke yi wajen ganin ta ƙara tsaftace zaɓe a Najeriya.

Tun farkon naɗa Farfesa Mahmood Yakubu Shugaban INEC, ya sha amsa gayyatar Majalisar Dattawa, inda ya ke ƙara jaddada buƙatar ƙara wa INEC ƙarfin iko, ta yadda za ta samu ƙwarin guiwar sake nazari da bin-diddigin sakamakon zaɓen da ta ke ganin an yi ƙwange ko harƙalla ko wuru-wuru ko haɗa-baki da wasu malaman zaɓe.

Kudirin Zaɓe na 2021, wanda INEC ke tunanin zai ba ta wannan ƙarfin iko, ya zo da akasin haka, idan sai ba Majalisar Dattawa ta canja tunanin ta ba.

Sashe na 65 na Kudirin Dokar Zaɓe na 2021 ya saɓule wa INEC ƙarfin ikon sake bin-diddigin sakamakon zaɓen da jami’in zaɓe ya rigaya ya bayyana, ko da kuwa da ƙarfin tuwo aka tirsasa shi, ko da ƙarfin bakin bindiga ko kuma ƙarfin aljihun ɗan takara.

Share.

game da Author