Mai Shari’a Nyako ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu, saboda ta fara hutu kuma ba a kai gogarman a gaban ta ba

0

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu sai bayan watanni uku.

Babbar Mai Shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa ta ɗage ci gaba da shari’ar sai ranar 21 Ga Okotoba, saboda alƙalai sun fara hutu daga yau Litinin, kuma ba a gabatar da Nnamdi Kanu a gaban ta ba.

Sai dai kuma mai gabatar da ƙara M.A Abubakar ya shaida wa kotu cewa mai yiwuwa ne jami’an SSS sun haɗu da wani ɗan cikas ne, domin su ke da alhakin gabatar da shi kotu, tunda a hannun su ya ke.

Amma kuma lauyan da ke jagorantar sauran lauyoyin Kanu, mai suna Ifeanyi Ejiofor ya ƙaryata Abubakar, inda ya yi zargin cewa an ɗauke Kanu, an fitar da shi daga Abuja.

Shari’ar ta yi tsaye cak tun a watan Afrilu, 2017 bayan ya tsallake katangar beli ya gudu a cikin watan Satumba, lokacin da sojoji su ka kai farmaki a gidan sa cikin watan Satumba, 2017.

An kamo Nnamdi Kanu a ƙarshen Yuni, 2021. An kai shi kotu a ranar 29 Ga Yuni, inda Mai Shari’a Binta Nyako ta bada umarnin a ci gaba da tsare shi zuwa yau, 26 Ga Yuli, shari’ar da yau ɗin ma ba a zauna an ci gaba ba.

Share.

game da Author