MAI LAYA KIYAYI MAI ZAMANI: Dala ta yi wa naira duka da gora mai kaca, kwana ɗaya bayan rataya mata laƙanin ki-bugu

0

Kwana ɗaya bayan da Bankin CBN ya bijiro da hanyoyin ƙara wa naira ƙarfi a kasuwannin hada, ciki har da daina sayar da dala ga ‘yan canji, a yanzu dala ɗaya ta tashi daga naira 504 zuwa naira 522.

PREMIUM TIMES HAUSA ta leƙa shafin yanar gizo na ‘yan canjin kuɗi, mai suna abokiFX.com inda su ka bayyana farashin duk dala ɗaya kan naira 522 a ranar Laraba, tun wajen 12 na rana.

PREMIUM TIMES ta buga yadda darajar naira ta ƙara zubewa tun a ranar Talata, ranar da Bankin CBN ya hana sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje.

Darajar naira a kasuwar tsaye ta ‘yan canji ta ƙara yin warsas a ranar da Babban Bankin Najeriya, CBN ya bada sanarwar daina sayar wa ‘yan canji dala da sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.

A yanzu dalar Amurka ɗaya daidai ta ke da naira 505 a kasuwar ‘yan canji, kamar yadda shafin yanar gizon bayanan canji a Lagos, mai suna abokiFX.com ya nuna a yammacin ranar Talata.

CBN ya bada dalilai da yawa da ya sa ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje, ciki har da zargin ana bi ta hannun su ana harƙallar karkatar da kuɗaɗe, lamarin da ke ƙara tauye tattalin arzikin ƙasa.

Bankin CBN ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje, a ƙoƙarin da ya ce ya ke yi domin daidaita darajar naira da ta tattalin arzikin ƙasar nan.

Babban Bankin Najeriya CBN ya bada sanarwar daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen waje kai-tsaye.

Shugaban Bankin CBN, Godwin Emefiele ne ys sanar da haka a ranar Talata a Abuja, bayan taron kwanaki biyu da Majalisar Tasarifin Tsare-tsaren Kuɗaɗe ta CBN ta gunadar.

Emefiele ya ce daga yau CBN zai riƙa sayar da dala d sauran kuɗaɗen waje ga bankunan kasuwanci kaɗai, ba ga ‘yan canji ba.

“Kuma CBN daga yau babu ruwan sa da shiga sha’anin yi wa kamfanonin ‘yan canji rajista.”

Ya ce wannan tsari da su ka ɗauka zai taimaka ƙwarai wajen ƙara wa naira ƙarfi da daraja a gaban idon kuɗaɗen ƙasashen waje.

CBN ya ce ya lura ana amfani da ‘yan canji ana karkatar da kuɗaɗen da ya kamata a ce an zuba su ne a jarin bunƙasa kasuwanci da tattalin arzikin cikin gida.

Daga nan sai ya ce duk mai son kuɗaɗen waje ya je wurin bankunan kasuwanci ya riƙa saye.

Sannan ya gargaɗi bankuna cewa duk wanda ya haɗa baki da ‘yan canji, za a yi masa hukuncin da sai ya yi da-na-sani.

Ya kuma gargaɗi ƙungiyoyin ƙasashen ƙetare waɗanda ya zarga da karkatar da kuɗaɗe ta hannun ‘yan canji, cewa su daina. Duk wanda aka kama, za a kai rahoton sa a gwamnatin ƙasar su.

PREMIUM ta buga labarin yadda wani masanin hada-hadar kuɗaɗe ya roƙi Bankin CBN ya rataya wa naira layar laƙanin hana ta firgita idan ta yi ido-biyu da dala a kasuwannin hada-hada.

Wani masanin ƙabali da ba’adin harkokin kuɗaɗe, Okechukwu Unegbu, ya roƙi Babban Bankin Najeriya (CBN) ya lalubo hanyoyin da zai saisaita tsadar kayan abincin da kayan masarufi ta hanyar dakatar da yawan farfaɗiya da faɗuwar ‘yan bori da naira ke yi a kasuwannin hada-hada na ciki da wajen ƙasar nan.

Okechukwu ya ce tsadar kayayyaki na ƙara tsananta cikin ƙasa, saboda darajar naira na ci gaba da taɓarɓarewa, sannan kuma a waje ko cikin gida duk inda naira ta yi ido-biyu da dala, sai ta fara karkarwa ta na firgita.

Okechukwu wanda shi ne tsohon Shugaban Ƙungiyar Mashahuran Masana Harkokin Kuɗaɗe na Cibiyar CIBN ta Najeriya, ya bada wannan shawara ce a ranar Lahadi, a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Ya ƙara da cewa yawan karyewar darajar naira da ake fuskanta abin damuwa ne, domin yanzu akwai wasu sinadarai da su ka kamata a yi amfani da su, wajen ƙara wa naira ƙarfi ta daina yawan firgita ko faduwar-‘yan-bori.

“Ya kamata Kwamitin Tsare-tsaren Ka’idojin Hada-hadar Kuɗaɗe na CBN ya yi nazarin shingayen da za a gindaya wa naira, matsayin kan iyakar da za a hana ta tsallakewa, kamar yadda bankin ya yi sau shida a baya.

“Har yanzu tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki na hauhawa a Najeriya. Ƙuɗaɗen ruwan da bankuna ke bayarwa kuma sai hawa-da-sauka su ke yi. Sannan kasuwar canjin kuɗaɗen waje kuwa a nan ne aka fi yi wa naira laga-laga ko da kallo ta je, ballantana ta je cin kasuwar.

“Yanzu kusan naira 500 ce daidai da dala 1. A Najeriya idan ka na da naira 500, za ka iya cin abinci garau-garau har a jefa maka ‘yar tsokar nama. To inda tsiyar ta ke, idan ka je Amurka a can dala 1 babu abin da za ta yi maka.”

A ƙarshe ya bada shawarar cewa a yanzu da farashin ɗanyen mai ya yi sama a kasuwar duniya, ya kamata Kwamitin MPC na Bankin CBN ya bijiro da tsarin da zai samar da ayyukan yi sosai a ƙasar nan.

Share.

game da Author