LUWAƊI: Ƴan sandan Katsina sun kama wasu mutum 5 da suka rika yin lalata da wani ɗan shekara 17

0

Kakakin rundunar ƴan sandan Katsina Gambo Isa ya bayyana cewa rundunar ta kama wasu mazaje su biyar da suka rika yin lalata da wani ɗan saurayi mai shekaru 17.

Waɗannan mazaje suna yin lalata da wannan yaro ne ta dubura a wurare da bam da bam.

” Akwai ɗaya daga cikin su da ya rika yi wa yaron barazanar zai kashe shi idan ya faɗa wa wani a duk ranar da ya sadu dashi.

An kama matar kasurgumin ɗan bindiga da miliyan biyu a jakanta

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina Gambo Isah ya bayyana yadda jami’an ƴan sanda suka damke matar wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wa jihar.

Isah ya ce an kama matar Murnai a bisa babur bayan ta dawo daga Kaduna inda ta je harkar karbar kuɗin fansa.

” An kama mai ɗakin Nura Murnai bayan ta dawo daga Kaduna wajen amsar sakon miliyan biyu daga wurin wani abokin harkar mijin ta, Nura Murnai.

” Da aka bincike ta an samu naira miliyan 2 a cikin jakan ta.

Isah ya kara da cewa iata da kanta ta tabbatar wa ƴan sanda cewa ta na yinwa majinta zirga-zirgar amsar kuɗaɗe daga wurare.

Nura Murnai ya shahara wajen satar mutane da harkallar bindigogi wanda ake nema ruwa a jallo.

Share.

game da Author