1. Farkon bayyanar Sunday Igboho a matsayin gogarman shelanta korar Fulani makiyaya daga yankin Yarabawa, PREMIUM TIMES Hausa ta kawo cikakken rahoton yadda jigon Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya yi amfani da shi da gungun ‘yan iskan sa wajen cin zaɓe a yankin.
2. Sunday Igboho tun kafin haɗuwar sa da Bola Tinubu, ya kasance tantagaryar ɗan daba da jagaliyar siyasa. Shi da yaran sa ake ɗauka matsayin sojan-haya a yankin Yarabawa, domin a ci zaɓe da tsiya ko da tsinin-tsiya.
3. Sunan Sunday Igboho, mazaunin garin Ibadan a Jihar Oyo, ya fito a faɗin ƙasar nan bayan da a farkon shekarar nan ya ayyana korar Fulani makiyaya daga jihohin Yarabawa baki ɗaya.
4. Sunday Igboho ya ja zugar ‘yan takifen Yarabawa matasa su ka kai wa Fulani mazauna Igangan hari.
5. Wanan hari sun banka wa gidan Sarkin Fulanin Igangan wuta, aka ƙona masa motoci kuma aka kashe ɗan sa.
6. Su Sunday Igboho sun fatattaki Sarkin Fulanin Igangan daga Jihar Oyo, ya yi ƙaura zuwa Jihar Kwara, jihar sa ta asali.
7. Sunday Igboho ya ayyana tawayen ɓallewa daga Najeriya, ya raɗa sunan sabuwar ƙasar da ya kafa, “Yoruba Nation”. Kuma ya ɗaga tutar ƙasar ta sa a sama duk duniya an gani.
7. Ya yi faifen bidiyo inda ya yi barazanar buɗe dukkan kan iyakokin Najeriya da ke Kudu maso Yamma, saboda a cewar sa, yanzu kan iyakokin ba a ƙarƙashin Najeriya su ke ba, su na a ƙarƙashin ƙasar “Yoruba Nation.”
8. Magoya bayan ka ɗauke da ƙyallaye masu hotunan ka, sun darkaki kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, a Idiroko, Legas, inda su ka ƙwace bindigogi daga hannun jami’an kwastan.
9. Yaran ka sun riƙa dukan jami’an kwastan a Idiroko kuma su ka riƙa rekodin ɗin bidiyon dukan da su ke yi masu.
10. Har yau Sunday Igboho bai fito a jaridu ko ya yi bidiyon da ya nesanta kan sa da abin da yaran sa su ka yi wa jami’an kwastan a Idiroko ba.
11. Ka fito a bidiyo ka umarci matasa masu goyon bayan ka cewa su ɗauki makamai. Ka ce idan ba su san inda ake sayarwa ba, to kai ka sani, za ka iya yin oda ko guda nawa ne ka kawo domin kowa ya samu.
12. Sunday Igboho ya ce babu wanda ya isa ya hana shi ɗaukar makamai.
13. Ya yi faifan bidiyo ka watsa, inda ya yi kurarin cewa ko jami’an tsaro 1,000 su ka je kama shi, to sai sa’ar gaske 1,00 daga cikin su za su iya komawa gida da ran su.
14. Jami’an DSS sun gano cewa bindigogin da ‘yan iskan yaran Sunday Igboho su ka ƙwace a hannun jami’an kwastan su na gidan ka na Badun an ɓoye.
14. DSS sun kai farmaki gidan Sunday Igboho cikin dare, an yi musayar wuta da yaran sa waɗanda ke kwana a gidan.
14. Wata mata mai suna Lady K da ta kwana a gidan a wannan daren, ta riƙa yin bidiyo ta na furta cewa, sojoji ne su ka kai farmaki a gidan Igboho.
15. Lady K ta riƙa watsa bidiyo, ta na kiran magoya bayan Sunday Igboho su kai masa ɗaukin musayar-wuta da jami’an tsaro.
16. Jami’an DSS sun yi sanarwar Sunday Igboho ya kai kan sa ofishin ‘yan sanda, amma sai ya gudu.
17. Sunday Igboho ya tsare zuwa Kwatano, inda jami’an tsaron Jamhuriyar Benin su ka damƙe shi.
18. Sunday Igboho ya riƙa bi jihohin Yarabawa ya na bai wa makiyaya har da waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, wa’adin ficewa daga yankunan jihohin Yarabawa.
19. Sunday Igboho ya ce babu wanda ya isa ya kama shi.
20. Sunday Igboho ya samu fasfo ɗin Najeriya ta ɓarauniyar hanya a Jamhuriyar Benin.
21. Sunday Igboho ya rura wutar gaba, ƙiyayya a tsakanin ‘yan Najeriya, dunƙulalliyar ƙasa ɗaya mai al’umma ɗaya a siyasance.
Mai yiwuwa dukkan waɗannan canje-canjen ne mai gabatar da ƙara zai yi amfani da su wajen gurfanar da Igboho gaban mai shari’a a kotu, idan Jamhuriyar Benin ta damƙa wa Najeriya shi.
Discussion about this post