Karamar ministar Abuja Ramatu Tijjani Aliyu ta bayyana cewa cutar kwalara ta yi ajalin mutum 54 a gundumomi 6 dake babban birnin tarayya Abuja.
Ramatu ta faɗi hake ne a taron wayar da kan mutane game da cutar da aka yi a fadan Agora sarkin Zuba Alhaji Mohammed Bello Umar ranar Asabar.
Ta ce yin haka ya zama dole ganin yadda cutar ke ci gaba da yaɗuwa a duka gundumomin dake babban yankin.
Ramatu ta ce sakamakon gwajin cutar da aka yi wa mutum 604 ya nuna cewa mutum 9 sun kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 54 a babban birnin tarayya.
Ta yi kira ga mutane da su tsaftace muhallin su da abincin da suke ci domin guje wa kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba a makon jiya PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin cewa mutum 8 sun kamu da cutar a Abuja.
Hukumar kula da hukumar babban birnin tarayya Abuja ta gano haka bayan gwajin jinin mutum 514 da aka yi ranar 8 ga Yuli 2021.
Yaduwar cutar kwalara a Najeriya
PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin cewa mutum 289 sun kamu da cutar daga watan Janairu zuwa Yuni a kasar nan.
Hukumar NCDC ta ce an gano wadannan mutane a jihohi 8 a Najeriya.
Wadannan jihohi sun hada da Filato, Bauchi, Gombe, Kano, Zamfara, Bayelsa da Kaduna.
Hukumar ta ce zuwa yanzu cutar ta yadu zuwa jihohi 13 a kasar nan.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.
likitoci sun yi kira da arika gaggauta garzaya asibiti domin warkar da cutar.
Discussion about this post