Kungiya mai zaman kanta ‘MAP Donation International’ ta tallafa wa fannin kiwon lafiyar jihar Bauchi da magungunan kashe kwayoyin cututtuka (Antibiotics) har na naira biliyan 10.
Mai taimakawa gwamnan jihar Bala Mohammed kan lamuran bangarorin da dama Alhaji Isa Sale ya sanar da haka ranar Alhamis.
Sale ya ce daga cikin maganin kashe kwayoyin da kungiyar ta bada akwai alluran maganin ‘Daptomycin’ wanda zai taimakawa wajen kashe cututtuka da dama a jihar.
Ya ce kungiyar ta bada magungunan ne domin tallafa wa gwamnati kan kokarin da ta ke yi wajen dakile yaduwar cututtuka a jihar musamman cutar korona, shawara da sauran su duk da cewa gwamnatin na fama da karancin kudade.
Sule ya ce kungiyar ‘MAP Donation international’ ta hada hannu da gidauniyar ‘Reed Foundation’ domin bada gudunmawar wasu magungunan kashe kwayoyin cututtukan domin kashe cututtukan hawan jini, ciwon siga, daji, cututtukan dake kama mamumfashi da sauran su a jihar.
“Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta za ta tallafa wa jihar da magungunan inganta lafiyar mata masu ciki guda 180,000 domin rabawa mata masu ciki a jihar kyauta.
Bayan haka a madadin sarakunan gargajiya na jihar sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu ya mika godiyarsa ga kungiyoyin da suka tallafa wajen inganta fannin kiwon lafiyar jihar.
Bilyaminu ya ce sarakunan gargajiya za su sa Ido domin ganin an yi amfani da wadannan magunguna ta hanyoyin da ya kamata musamman a yankin karkara.
Gwamna Mohammed ya ce gwamnati za ta tabbatar an raba magungunan mutane sun samu.
Ya ce gwamnati za ta raba magungunan a manya da kananan asibitocin gwamnati a jihar sannan za a kafa kwamiti domin ganin an yi amfani da magungunan ta hanyoyin da ya kamata.
Mohammed ya ce gwamnati ta fara gyaran manyan asibitocin gwamnati guda 14 tare da kara yawan gidajen likitoci a jihar.
“Gwamnati za kuma ta karo kwararrun likitoci domin samar da lafiya ta gari wa mutane a jihar.
Kungiyar ‘MAP Donation International’ kungiya ce dake bada tallafin magunguna domin inganta lafiyar mutane a fadin duniya.
Discussion about this post