Gwamnonin Kudu sun yi fatali tare da nuna ƙin amincewa da kashi 3% bisa 100% da kudirin wanda Majalisar Tarayya ta amince a riƙa bai wa yankunan da ake haƙo fetur ɗin.
A cikin wata sanarwar manema labarai da Gwamnonin Kudu su ka bayar bayan tashin su daga taro a Legas a ranar Litinin ɗin nan, gwamnonin sun ce kamata ya yi a riƙa ware masu kashi 5% bisa 100%.
Sai dai kuma gwamnonin sun yaba wa majalisar dangane da irin namijin ƙoƙarin su wajen gama duba ƙudirin dokokin da wuri, har su ka damƙa ta gaba.
Bayan ɗaukar shekaru masu yawa ba a miƙa wa Shugaban Ƙasa ƙudirin ba, a yanzu an tantance shi kuma majalisar tarayya da ta dattawa sun zartas da a riƙa bai wa wasu jihohin Arewa har kashi 30% bisa 100%.
Wannan l’amari dai ya harzuƙa ‘yan Yankin Neja, har Dattijo Edwin Clerk ya yi barazanar cewa za su hana haƙo ɗanyen mai yankin Naja Delta.
Haja kuma an samu saɓani dangane da hakkin mallakar kamfanin NNPC Limited.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga barazanar Edwin Clerk, wanda ya ce Yankin Neja Delta zai hana haƙo ɗanyen mai a Najeriya saboda ƙudirin dokar ribar fetur ta fifita wasu jihohin Arewa kan jihohin da ake haƙo mai.
Dattijo mai faɗa a ji a yankin Neja Delta, ya bayyana cewa za su hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai su ci gaba da aiki a yankin Neja Delta, matsawar dai ba a dawo da kudirin raba ribar man fetur da Majalisa za ta gabatar ba.
Clerk ya ce ‘Yan Majalisar Dattawa da na Tarayya sun raina wa al’ummar Yankin Neja Delta wayau, saboda sun soke kason kashi 10 bisa 100 da za a riƙa ba Neja Delta, su ka maida shi kashi 3 bisa 100, sannan su ka lafta wa wasu jihohin Arewa har kashi 30 bisa 100.
Ya kira wannan ƙudiri da cewa, ƙudirin iya shege ne da shaiɗanci da kuma tantagaryar rashin adalci.
“Lokacin Daina Yi Mana Mulkin Mallaka Ya Yi” -Edwin Clerk
“Mu na gargaɗin cewa jama’ar Neja Delta da an kai su bango. Tutar ta isa haka. Mun gaji da irin mulkin da ake yi mana mai kama da mulkin mallaka, wanda ‘yan uwan mu da abokan mu ‘yan Arewa ke yi mana.
“A yau ragamar harkokin fetur a ƙasar nan ta na hannun ‘yan Arewa, duk da dai harkokin yaƙi man kamfanonin ƙasashen Turai ne ke gudanarwa a madadin Gwamnatin Tarayya.” Inji Clerk.
Dattijo Clerk wanda shi ne jagoran wata ƙungiyar kare muradun Neja Delta, PANDEF, ya ce shi da sauran ɗaukacin dukkan ‘yan Neja Delta sun ƙi amincewa da kason cikin cokali na kashi 3 bisa 100 na ribar mai da za a ba yankin Neja Delta sa kuma kashi 5 cikin 100 da aka ware wa NNPC Limited da za a rika bai wa al’ummar yankin da ake haƙo man.
“Idan ba a yi mana haka ba kuwa, to ya zama tilas mu tashi tsaye mu fito mu ƙwaci haƙƙin mu da tsiya-tsiya. Kuma sai mu hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai ci gaba da aikin haƙar mai a yankin mu.”
Discussion about this post