Kotun Ƙoli ta umarci Gwamnatin Najeriya da hukumomin da ke da alaƙa da harkar fetur cewa kada a damƙa wa Jihar Imo wasu rijiyoyin danyen mai 17.
Rijiyoyin dai su na a yankin Akri da Mgbede ne da ke maƙwautaka da jihar Ribas, kuma jihohin biyu sun daɗe su na tankiya a kan rijiyoyin.
A ranar Laraba ce Kotun Ƙoli a ƙarƙashin hukuncin da ta yanke, ta ce kada a damƙa wa Jihar Imo rijiyoyin, har sai an ji hukuncin da ta yanke, dangane da ƙarar da Jihar Ribas ta shigar kan rijiyoyin 17 tukunna.
Lauyan Jihar Ribas mai suna Emmanuel Ukala ne ya shigar da ƙarar amincewar, a madadin Gwamnatin Jihar.
Kotun Ƙoli ta aika wa Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma ta aikawa Hukumar Raba Arzikin Ƙasa cewa kada su sake su raba wa Jihar Imo kason waɗannan rijiyoyi a cikin kason kuɗaɗen da ake bai wajihohi a ƙarshen wata tukunna.
Shi ma Ministan Shari’a Abubakar Malami an yi masa irin wannan gargaɗi.
An sa ranar 21 Ga Satumba, domin bayyana wanda ke da haƙƙin mallakar rijiyoyin.
Discussion about this post