Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ce tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe Kemi Adeosun ba ta yi wani laifi ba don an naɗa ta Minsiatar Harkokin Kuɗaɗe cikin 2015 ba tare da halartar aikin bautar ƙasa (NYSC) ba.
Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya ce ba ta buƙatar gabatar da katin shaidar bautar ƙasa (NYSC), domin a lokacin da ta kammala jami’a cikin 1989 ta rigaya ta zama ‘yar Birtaniya.
“Kuma lokacin da ta dawo Najeriya ta haura shekaru 30, ƙa’idar waɗanda aka tilasta wa zuwa aikin bautar ƙasa.”
Sai dai kuma kotu ba ta ce komai a kan batun fojare na sarifiket na NYSC na jabu da Kemi Adeosun ta yi ba, kuma ta gabatar da shi a lokacin da za a naɗa ta Ministar Harkokin Kuɗaɗe.
Sannan kuma ba a tayar da maganar yadda ta riƙa dumbuza wa ‘yan majalisa maƙudan kuɗaɗe ba, a lokacin da su ka gano ta yi fojare na shaidar NYSC.
PREMIUM TIMES ce ta fallasa Kemi Adeosun kuma ta riƙa bibiyar harƙallar, har Kemi ta gaji ta ajiye aiki.
Sai dai kuma bayan ta ajiye aiki, Shugaba Muhammadu Buhari ya gode mata, maimakon ya sa a hukunta ta.