Kotu ta gurfanar da wasu ma’aikata 4 da suka ci amanar abokin aikin su, suka rika lalata da ya’yan sa biyu

0

Kotu dake jihar Legas ta gurfanar da wasu ma’aikatan kamfanin ‘Kazmus Nigeria Ltd’ da suka ci amanar abokin aikin su suka rika lalata da ‘ya’yan abokin aikinsu biyu.

Kotun ta gurfanar da Ojo Taiye mai shekara 35 kuma direba, John Mohasan mai shekara 24 mai fadi, Peter Arabo mai shekara 33 lebura da Adenekan Adedeji mai shekara 40 direba bisa laiffuka uku.

Yaran da wadannan maza suka yi lalata da su na da shekaru 5 da 3 a lokacin.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta bayyana cewa an fara gurfanar da wadannan maza agaban alkali Sybil Nwaka a ranar 28 ga Afrilu 2018 sannan ko a lokacin mazan sun musanta laifin da ake zargin su da shi.

Nwaka ya yanke hukuncin daure wadannan maza a kurkuku har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar.

Sai dai kafin a yi hakan an canja wa Nwaka wurin aiki zuwa kotun daukaka kara a jihar.

A yanzu an gurfanar da wadannan mutane ne a gaban wani alkalin dabam wato Rahman Oshodi.

“Abokin aikinsu kuma mahaifin yaran kan kawo ‘ya’yan sa mata biyu wurin aiki bayan an taso su daga makaranta, idan ya tashi aiki sai su koma gida tare.

“A duk lokacin da mahaifan yaran ya kawo ‘ya’yansa sai wadannan abokan aikin sa su zauna da yaran suna wasa da su zuwa ya tashi aiki. Ashe lalata suke yi da su idan ya ajiye su.

Share.

game da Author