Kotu ta ɗaure wani matashi da ya shahara wajen fashin wayar mutane da dare

0

Kotun majistare dake jihar Legas ta ɗaure Yinka Olamilekan mai shekaru 19 a kurkuku bayan ya yi wa wani fashi da adda a jihar.

Kotun ta gurfanar da Olamilekan bisa laifin yin fashin waya.

Alkalin kotun O.O. Fajana ya yi watsi da rokon sassauci da Olamilekan ya nema, ya ce za a daure shi a kurkuku har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka dake jihar.

Za a ci gaba da Shari’a ranar 18 ga Agusta.

Ɗan Sandan da ya shigar da ƙarar Kenrich Nomayo ya ce Olamilekan tare da wasu abokansa sun kwace wa Aminu Zaki wayar salulansa mai kiran ‘Camon16’ da kudinsa zai kai Naira 75,000 da katin ATM dinsa guda biyu.

Nomayo ya ce Olamilekan ya aikata wannan fashi ne a ranar 20 ga Yuli da misalin karfe 9:30 na dare a titin Alfa Nla Agege.

Ya ce Olamilekan ya shiga hannun jami’an tsaro bayan Aminu ya rangaɗa ihun neman taimako daga mutane.

“Bayan Aminu ya yi ihun ne abokan Olamilekan suka arce suka barshi bayan jama’an gari sun diran musu.

Share.

game da Author