Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 146 sun kamu da cutar korona sannan cutar ta yi ajalin mutum daya daga ranar Litini zuwa Laraba a kasar nan.
Alkaluman da hukumar ta fidda ranar Litini sun nuna cewa jihar Legas ta fi yawan samun mutanen da suka kamu da mutum 40, Yobe – 10, Rivers -5, Oyo – 4 da Kano- 2.
Sannan na ranar Talata sun b Kaduna – 3, Oyo -3, Filato-3, Rivers-2 da Ogun -1.
Zuwa yanzu mutum 167,618 ne suka kamu, mutum 2,120 sun mutu a dalilin cutar.
A ranar Laraba Legas -47, Gombe -15, Abuja -4, Rivers -4, Kaduna -3 da Ekiti -3.
Mutum 164,244 sun warke sannan har yanzu akwai mutum 1,254 dake dauke da cutar a kasar nan.
Hukumar NPHCDA ta bayyana cewa an yi wa mutum miliyan 3.2 allurar rigakafin korona a kasar nan.
A ranar Litini gwamnatin tarayya ta saka kasar Afrika ta Kudu a jerin kasashen da ta hana mutane daga kasar nan zuwa sannan da mutane daga can sauka a Najeriya saboda yaduwar sabuwar samfurin korona dake yi wa mutane kisan fard-daya wato ‘Delta Variants’.
Gwamnati ta kuma ce sai fasinjoji ‘yan Najeriya da suka dawo daga kasar sun kiyaye dokokin Korona da aka saka kafin a bari su shiga garuruwan kasar nan.
Gwamnati ta yanke wannan hukunci ne saboda fitinar da ta hango na shigowa da cutar ƙasa nan.
Discussion about this post