KORONA: Sama da mutum 100 sun kamu ranar Laraba a Najeriya

0

Cutar Korona da ake wa ganin yanzu dai sai gangara, tana neman ta dawo sabuwa a Najeriya.

An kai ga a wasu ranakun ma ba a samun ko mutum ɗaya da ya kamu da cutar sai kuma gashi yanzu abun da neman ya dawo gadan-gadan.

Najeriya ta fara wuce mutum 100 da suka kamu da cutar.

A alƙaluman da hukumar NCDC, ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa mutum 110 ne suka kamu da cutar a jihohi bakwai har da Abuja.

Kusan wata biyu kenan rabon da Najeriya ta bayyana yawan mutanen da suka kama sun wuce 100.

Mutum 88 suka kamu a jihar Legas.

Zuwa yanzu mutum 164,408 sun warke daga cutar a Najeriya, bayan sun kamu sanna akwai mutum sama da 1300 da ke dauke da cutar a Najeriya yanzu.

A wajen rigakafi kuma, an yi wa mutum sama da miliyan biyu alluran rigakafin cutar zuwa yanzu a kasar nan.

Share.

game da Author