KORONA: Mutum 74 sun kamu mutum daya ya mutu a Najeriya ranar Alhamis

0

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 74 sun kamu sannan mutum daya ya mutu a ranar Alhamis.

Zuwa yanzu mutum 167,692, sannan mutum 2,121 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.

Alkaluman da hukumar ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa jihar Legas ta fi yawan samun mutanen da suka kamu da mutum 49, Ondo-13, Oyo-3, Rivers-3, Kaduna-1, Ekiti-1, Gombe-1, Jigawa-1, Ogun-1 da babban birnin tarayya Abuja-1.

An sallami mutum 164,273 sannan har yanzu akwai mutum 1,300 dake dauke da cutar a kasar nan.

Hukumar NPHCDA ta bayyana cewa an yi wa mutum miliyan 3.2 allurar rigakafin korona a kasar nan.

Daga ranar Litini zuwa Laraba mutum 146 sun kamu da cutar korona sannan cutar ta yi ajalin mutum daya a kasar nan.

Bankin Bada Ramce na Duniya (IMF), ya bayyana cewa hanya mafi sauki da kuma wahala da ita ce kaɗai Ƙasashen Kudancin Sahara za su bi domin hana sabuwar korona mai suna Delta ɓarkewa a yankin su, ita su hanzarta aikin yi wa jama’a ba adadi allurar rigakafin korona kawai.

Haka kuma a wani rahoton IMF, Ƙasashen Kudancin Sahara na fuskantar ɓarkewar sabuwar korona mai suna ‘Delta, wadda ta fi korona biyu da aka yi baya saurin lahanta mutane da kashe su.

Share.

game da Author