KORONA: Da ka ƙi yin rigakafi gara a ɗirka maka, ba kowa allurar ke wa illa ba – WHO

0

Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO), ta ƙara nanata cewa yin allurar rigakafin korona ya fi rashin yin ta alfanu, domin waɗanda rigakafin ke haifar wa ‘yan matsaloli ba su fi kwatankwacin yawan ruwan da aka ɗebo a cikin cokali da ga cikin teku ba.

Masana a WHO sun ce yin allurar ya na da fa’ida sosai, domin ya na rage adadin yawan waɗanda ake kwantarwa asibiti da kuma rage yawan mutuwa daga kamuwa da cutar korona da kuma baza cutar.

“Duk da ‘yan rahotannin haddasa illa ko illoli a jikin wasu ɗaiɗaikun mutane ƙalilan, yin rigakafin korona ya fi rashin yi fa’ida.”

Fama Da Zafi Da Kumburin Zuciya Bayan Ɗirka Wa Mutum Rigakafi:

WHO ta yi wannan bayani ne biyo bayan ɗaiɗaikun rahotannin da aka riƙa samu daga waɗanda su ka yi fama da lalurorin kumburin zuciya ko zafi a zuciyar su ko kuma zuciyar ta ɗan koma ja (myopcarditis).

Akwai kuma ɗaiɗaikun mutane ƙalilan da su ka bada rahoton fama da kumburi ko zafin zanen tantanin da ya kewaye zuciyar su (pericarditis).

Sun bayyana cewa sun yi fama da waɗannan lalurorin ne bayan an ɗirka masu rigakafin allurar Pfizer da kuma waɗanda su ka ce bayan an yi masu rigakafin allurar Moderna su ka samu lalurorin.

Yayin da a wasu lokuta matsalar kan tsananta, amma dai akasari ɗan zafin da akan ji na ɗan wani lokaci ne ƙalilan, kuma da an hanzarta magance shi, shikenan.” Haka dai Kwamitin Mai Bayar da Shawarwari ga WHO kan Rigakafi ya bayyana.

Wani rahoto da aka tattara a Amurka ya nuna mutum 40 ne kaɗai a cikin mutum miliyan ɗaya su ka samu matsala a lokacin da aka yi masu rigakafin korona zagaye na biyu a cikin maza.

A cikin mata miliyan 1 kuma, mace 4 ce kaɗai ta yi fama da lalura.

Haka dai rahoton binciken ya nuna, wanda aka fitar a ranar 11 Ga Yuni, 2021.

An yi binciken ne tsakanin matasa ‘yan shekaru 12 zuwa 29, waɗanda aka ɗirks wa rigakafin allurar mRNA ta korona.

Amma da aka yi bincike tsakanin ‘yan shekaru 30 zuwa sama, an samu rahoton masu lalurori ga mutum biyu kacal a cikin maza miliyan ɗaya.

A cikin mata kuma miliyan ɗaya, su ma mace biyu kaɗai aka samu.

Idan An Haɗu Da Ciwon Ƙirjin Da Ya Ƙi Warkewa Bayan Rigakafi, A Garzaya Ga Likita:

Masana a Hukumar WHO sun bada shawarar cewa da zarar an fuskanci alamomin wasu lalurorin ciwon ƙirji ko wani zafin ya ƙi wartsakewa, ko alamomin da aka lissafa, to a garzaya wurin likita kawai.

Kada A Yi Wasa Da Sarƙewar Numfashi Ko Bugun-zuciya:

Shi ma wanda ya ji ya na samun wahalar yin numfarfashi bayan ɗirka masa Rigakafi, ko fama da bugun-zuciya, to ya garzaya ya ga likita.

Share.

game da Author