Kwamishinan ilimin Jihar Kaduna Shehu Muhammad ya bayyana cewa gwamnatin jihar bata canja ranar komawa makarantun Jihar ba.
Jaridu sun ruwaito tun ranar Litinin cewa gwamnatin jihar ta sanar da rufe makarantun jihar har sai llla-masha-Allahu.
Cewa wai gwamnan jihar ya sanar da haka a wani taro da yayi da shugaban kungiyar malamai da wasu shugabannin ƙungiyoyi a jihar na gaskiya bane.
Hwamnati ta ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai bai yi irin wannan taro da wasu ba da har ya furta rufe makarantun jihar har sai an gwamnati ta tabbatar da an samu tsaro a jihar ba.
Kwamishina Shehu ya ce makonni uku aka baiwa makarantun jihar kuma har yanzu akan haka gwamnati take.
Wasu malamai da suka tattauna da wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA, sun ce suna goyon bayan karin hutun idan shine zai samar da tsaro wa ƴaƴan su.
” Hakan da gwamnati zata yi idan ma ƙara kwanakin hutun makarantun zata yi, ba laifi bane domin zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki. Idan ɗan ka na makaranta hankalinka kwance ya fi. Saboda haka ayi karin hutu a samu lafiya a makarantun jihar yafi lafiya maimakon gaggawar komawa amma kuma hankali a tashe.
Wani malami Peter Sambo, shima ya tofa albarkacin bakin sa game da haka, inda ya ce makarantun jihar sun zama abin tsoro ga iyaye da ɗalibai.
Ya yi addu’ar Allah ya kawo karshen wannan matsala ta tsaro a kasar nan.
Har yanzu akwai ɗaliban makaranta sama 80 dake tsare a hannun ƴan bindiga suna jiran a biya su ƙudin fansa.
Discussion about this post